{"id":6378,"date":"2025-09-11T08:53:45","date_gmt":"2025-09-11T08:53:45","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6378"},"modified":"2025-09-11T08:53:45","modified_gmt":"2025-09-11T08:53:45","slug":"maaikatan-lafiya-a-zamfara-sun-fara-yajin-aikin-gargadi-na-mako-guda","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/maaikatan-lafiya-a-zamfara-sun-fara-yajin-aikin-gargadi-na-mako-guda\/","title":{"rendered":"Ma\u2019aikatan Lafiya A Zamfara Sun Fara Yajin Aikin Gargadi Na Mako Guda"},"content":{"rendered":"<p>Kungiyar Ma\u2019aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN), reshen Jihar Zamfara, ta ayyana yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai bisa zargin wariya a aiwatar da tsarin albashi na musamman na ma\u2019aikatan lafiya (CONMESS).<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar na jihar, Kwamared Shamsudeen Sadeeq ya sanya wa hannu, ma\u2019aikatan sun zargi Kwamishinar Lafiya, Dr. Nafisa Mohammed Maradun, da aiwatar da tsarin CONMESS kashi 100 ga likitoci kawai, tare da watsar da sauran ma\u2019aikatan lafiya.<\/p>\n<p>Kungiyar ta ce ta gudanar da tarurruka da dama da jami\u2019an gwamnati, ciki har da Kwamishinar Lafiyar, da Shugaban Ma\u2019aikata na Jihar da Kwamishinan \u2019Yan Sanda, amma duk ba su haifar da Da mai ido ba.<\/p>\n<p>Saboda haka kungiyar ta fara yajin aikin daga daren Laraba, 10 ga Satumba, zuwa 17 ga Satumba, 2025.<\/p>\n<p>MHWUN ta umarci mambobinta a cibiyoyin lafiya na matakin farko, asibitocin gwamnati da na musamman su shiga\u00a0 yajin aikin.<\/p>\n<p>Ta kuma gargadi cewa, idan gwamnati ta kasa magance koke-koken su a wadannan kwanaki, za su shiga yajin aikin sai Baba-ta-gani.<\/p>\n<p>A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta roki kungiyar ta janye yajin aikin, tana mai bayyana shi a matsayin abin da bai dace da lokaci ba, musamman duba da annobar amai da gudawa da ke addabar al\u2019umma.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da jami\u2019in hulda da jama\u2019a na ma\u2019aikatar lafiya, Suleiman Isah, ya fitar, Kwamishina Nafisa Maradun ta ce gwamnati ta sha alwashin inganta walwalar dukkan ma\u2019aikatan lafiya.<\/p>\n<p>Ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta amince da karin albashi ga likitoci a matsayin wani bangare na shirin inganta walwalar ma\u2019aikata.<\/p>\n<p>Kwamishinar ta musanta zargin nuna son kai, tana mai cewa tattaunawa na gudana da masu ruwa da tsaki domin samar da ingantaccen tsari ga dukkan ma\u2019aikatan lafiya.<\/p>\n<p>Dr. Nafisa Maradun ta bayyana rashin jin dadinta kan matakin yajin aikin, tare da kira ga kungiyar ta koma kan teburin tattaunawa, inda ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar a shirye take domin tattaunawa ta hanyar lumana don warware matsalolin da ke akwai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kungiyar Ma\u2019aikatan Lafiya ta Najeriya (MHWUN), reshen Jihar Zamfara, ta ayyana yajin aikin gargadi na kwanaki bakwai bisa zargin wariya a aiwatar da tsarin albashi na musamman na ma\u2019aikatan lafiya (CONMESS). A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar na jihar, Kwamared Shamsudeen Sadeeq ya sanya wa hannu, ma\u2019aikatan sun zargi Kwamishinar Lafiya, Dr. [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6381,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12,4],"tags":[1542,37,115],"class_list":["post-6378","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","category-lafiya","tag-maaikatan-lafiya","tag-yajin-aiki","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250911-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6378","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6378"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6378\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6382,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6378\/revisions\/6382"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6381"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6378"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6378"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6378"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}