{"id":6368,"date":"2025-09-10T22:56:01","date_gmt":"2025-09-10T22:56:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6368"},"modified":"2025-09-10T22:56:01","modified_gmt":"2025-09-10T22:56:01","slug":"jigawa-za-ta-kashe-naira-biliyan-daya-domin-kula-da-lafiyar-mutane-masu-rauni","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jigawa-za-ta-kashe-naira-biliyan-daya-domin-kula-da-lafiyar-mutane-masu-rauni\/","title":{"rendered":"Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan Daya Domin Kula Da Lafiyar Mutane Masu Rauni"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da biyan Naira Biliyan Daya domin ci gaba da bayar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mutane masu rauni dubu 287 a fa\u0257in jihar.<\/p>\n<p>Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim ka\u0257an bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Dutse, babban birnin jihar.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, wa\u0257anda za su ci gajiyar shirin sun ha\u0257a da yara, mata masu juna biyu, marasa galihu, tsofaffi da kuma masu nakasa a \u0199ar\u0199ashin shirin kula da lafiya na J-Basic Healthcare ga al\u2019ummar da ke da rauni a fadin jihar.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, majalisar ta kuma amince da \u0199ara yawan masu rijista daga 500 zuwa 1,000 a kowace mazaba.<\/p>\n<p>A cewarsa, Asusun tallafin lafiya na jihar muhimmin sashi ne na shirin J-Health Basic Social Insurance, wanda aka \u0199ir\u0199ira don kawar da cikas na ku\u0257i wajen samun lafiya ta hanyar \u0257aukar nauyin ku\u0257a\u0257en hidimomi ga wa\u0257anda ba za su iya biya ba.<\/p>\n<p>Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa, majalisar zartarwar ta amince da \u0199arin alawus alawus na kowane wata ga masu amfana da shirin tallafin malaman makarantu na J-Teach su 1,100, daga \u20a630,000 zuwa \u20a640,000 a matsayin wani \u0253angare na \u0199o\u0199arin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na \u0199ara wa malamai \u0199warin gwiwa, \u0199arfafa aiki da inganta ilimi a fadin jihar.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewa, amincewar ta biyo bayan bu\u0199atar da ma\u2019aikatar ilimi ta gaba da sakandare ta gabatar.<\/p>\n<p>Sagir ya ce, majalisar ta amince da kashe sama da Naira Miliyan 134\u00a0 domin biyan ku\u0257a\u0257en gudanarwa, harajin VAT, ku\u0257aden amincewa da guraben karatun dalibai, da ku\u0257in masauki ga \u0257alibai 15 na zangon karatu na 2025\/2026 a Jami\u2019ar Near East da ke Cyprus.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa, majalisar ta kuma amince da kashe sama da Naira Miliyan 152 domin ku\u0257in alawus alawus na inshorar lafiya, ku\u0257in takardun\u00a0 biza, da na izinin zama, da na abinci da kuma sufuri.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya \u0199ara da cewa, jimillar adadin ku\u0257a\u0257en da majalisar ta amince da su domin \u0257aliban 15\u00a0 ya kai sama da Naira Miliyan 286.7 na zangon karatun 2025\/2026.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da biyan Naira Biliyan Daya domin ci gaba da bayar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mutane masu rauni dubu 287 a fa\u0257in jihar. Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan jim ka\u0257an bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6369,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,4],"tags":[1539,1540,59],"class_list":["post-6368","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-j-health","tag-j-teach","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0045.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6368","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6368"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6368\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6370,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6368\/revisions\/6370"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6369"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6368"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6368"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6368"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}