{"id":6363,"date":"2025-09-10T22:26:28","date_gmt":"2025-09-10T22:26:28","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6363"},"modified":"2025-09-10T22:26:28","modified_gmt":"2025-09-10T22:26:28","slug":"uwargidan-shugaban-kasa-remi-tinubu-ta-kaddamar-da-gasar-muhalli-ta-miliyoyin-kudi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/uwargidan-shugaban-kasa-remi-tinubu-ta-kaddamar-da-gasar-muhalli-ta-miliyoyin-kudi\/","title":{"rendered":"Uwargidan Shugaban Kasa Remi Tinubu Ta Kaddamar Da Gasar Muhalli Ta Miliyoyin Kudi"},"content":{"rendered":"<p>Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta \u0199addamar wata gasa ta muhalli a fa\u0257in \u0199asa wacce aka \u0199ir\u0199ira domin \u0199arfafa dasa bishiyoyi, tsaftar muhalli da kuma rayuwa mai \u0257orewa a Nijeriya, a karkashin Shirin Ayyukan Jin Kai da Cigaban Al&#8217;umma (RHI).<\/p>\n<p>A yayin \u0199addamar da shirin a taron da take yi bayan watanni 3 da matan gwamnoni, wanda aka yi tare da shugabannin RHI na jihohi, Sanata Tinubu ta bayyana gasar a matsayin kira ga iyalai, \u0199ungiyoyin matasa, al\u2019ummomi da gwamnatocin jihohi da su ha\u0257a hannu wajen gina Nijeriya.<\/p>\n<p>Gasar wacce aka yi wa taken <em>\u201cA Inganta Yau Domin Gobe Ta Yi Kyau\u201d<\/em> ta kasu kashi uku, wacce kowannensu ke da lada mai tsoka:<\/p>\n<p>Gasa ta farko ita ce ta Iyali, wacce aka fi maida hankali kan jihohin Arewa 11 da sahara ta fi shafa, inda ake karfafa\u00a0 kowane iyali su dasa a\u0199alla bishiya \u0257aya, kuma wanda suka yi nasara za su kar\u0253i kyautar Naira miliyan 20.<\/p>\n<p>Haka kuma akwai rukuni na Al\u2019umma wanda aka bu\u0257e wa makarantu, \u0199ungiyoyin matasa, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma kananan hukumomi a fa\u0257in \u0199asa domin farfa\u0257o da wuraren da aka lalata, ta hanyar mai da su lambuna, filayen shakatawa ko wuraren muhalli. Wadanda suka yi nasara a wannan rukuni na\u00a0 kyautar Naira miliyan 50.<\/p>\n<p>Rukuni da karshe kuma na jihohi ne, amma banda Jihar Enugu, inda su kuma\u00a0 ake bukatar mai da\u00a0 hankali kan dasa bishiyoyi a tituna da manyan hanyoyi, wanda Jihar da ta fi nuna kulawa wajen kare muhalli za ta samu Naira miliyan 100.<\/p>\n<p>A wajen taron, Uwargidan Shugaban Kasar ta mi\u0199a takardar ceki na Naira miliyan 100 ga Jihar Enugu wacce aka za\u0253a a matsayin <em>\u201cJihar da ta yi fice a yawan bishiyoyi\u201d<\/em> saboda jajircewarta wajen dasa bishiyoyi da kuma tsaftar muhalli.<\/p>\n<p>\u201c<em>Enugu ta cancanci wannan<\/em>,\u201d in ji Sanata Remi Tinubu. \u201c<em>Ba wai kawai dasa bishiyoyi take ba, har da tsaftace muhalli. Idan ka shiga Enugu, kana ganin tsafta, wanda hakan abin a yaba ne matuka<\/em>.\u201d<\/p>\n<p>A matsayin wani \u0253angare na \u0199o\u0199arin RHI, ta bayyana cewa suna aiki tare da Ma\u2019aikatar Muhalli ta \u0198asa domin kafa kulob kulob na muhalli\u00a0 a makarantun sakandare da manyan makarantu, domin \u0257ora matasa kan sanin muhalli da kare shi.<\/p>\n<p>An tsara gasar <em>RHI Green Nigeria Challenge<\/em>\u00a0 har zuwa shekara ta 2026, inda aka riga aka kafa wa\u2019adin tura ayyuka. Ana kuma \u0199arfafa masu sha\u2019awar shiga gasar da su samu \u0199arin bayani kuma su tura ayyukansu ta manhajar shirin wato www.hrinitiative.org.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili\u00a0\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, ta \u0199addamar wata gasa ta muhalli a fa\u0257in \u0199asa wacce aka \u0199ir\u0199ira domin \u0199arfafa dasa bishiyoyi, tsaftar muhalli da kuma rayuwa mai \u0257orewa a Nijeriya, a karkashin Shirin Ayyukan Jin Kai da Cigaban Al&#8217;umma (RHI). A yayin \u0199addamar da shirin a taron da take yi bayan watanni 3 da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6366,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1538,66,1537,1536],"class_list":["post-6363","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-bishiyoyi","tag-gasa","tag-muhalli","tag-remi-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0241.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6363","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6363"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6363\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6367,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6363\/revisions\/6367"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6366"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6363"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6363"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6363"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}