{"id":6331,"date":"2025-09-10T10:00:27","date_gmt":"2025-09-10T10:00:27","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6331"},"modified":"2025-09-10T10:00:27","modified_gmt":"2025-09-10T10:00:27","slug":"gwamnatin-tarayya-zata-gabatar-da-shirin-wayar-da-kan-jamaa-game-da-muhimmancin-kisan-kasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-zata-gabatar-da-shirin-wayar-da-kan-jamaa-game-da-muhimmancin-kisan-kasa\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Zata Gabatar Da Shirin Wayar Da Kan Jama\u2019a Game Da Muhimmancin Kisan Kasa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin wayarda kan jama\u2019a game da Tattalin Arziki wanda zai inganta gaskiya, kishin \u0199asa, rikon amana da a duk wani abu na rayuwar \u0199asa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan yada labarai da wayar da kan jama\u2019a na kasa, Mohammed Idris ya bayyana haka a wajen bude taron Akanta na shiyyar Arewa na Minna 2025, wanda Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria ICAN ta shirya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ministan yada labarai da wayar da kan jama\u2019a na kasa, Malam Jibrin Baba Ndace, wanda ya samu wakilcin Darakta Janar na Muryar Najeriya, ya bayyana cewa wannan tsarin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai kaddamar nan ba da dadewa ba, an shirya shi ne don kokarin yaki da cin hanci da rashawa, ta hanyar magance ba kawai tsari ba, amma halayya da dabi\u2019un da ke dagula al\u2019amura.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mohammed Idris ya bayyana cewa, ba da lissafi shi ne ginshikin kowace al\u2019umma mai ci gaba, wanda idan ba shi da amincewar jama\u2019a ke rugujewa, cibiyoyi suna raguwa da ci gaba, a daya bangaren kuma, sake fasalin kasa yana magana ne kan dabi\u2019u, da\u2019a da kuma tsarin tunani na gama-gari wadanda suka daure mu yayin da mutane ke yin hakan tare da samar da taswirar dabi\u2019u da cibiyoyi da ake bukata don budo da dimbin arzikin dan Adam da abin duniya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mohammed Idris ya ci gaba da cewa, a matsayinsa na ministan yada labarai da wayar da kan jama\u2019a, aikin nasa ya samo asali ne wajen tsara kimar al\u2019umma, samar da amana ga gudanar da mulki da kuma wayar da kan \u2018yan kasa wajen cimma manufofin kasa daya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi gyare-gyaren da ke magana kai tsaye ga wannan batu, kamar shirin bayar da lamuni na dalibai da ke ba wa kowa damar samun ilimi mai zurfi, babbar hanyar Legas zuwa Calabar, babbar hanyar Badagry-Sakoto, gyara hanyar jirgin kasa ta Gabas.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Da yake sanar da bude taron, gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago, ya tabbatar wa mambobin Cibiyar Kula da Akantoci ta Najeriya cewa, daga cikin sama da Naira miliyan dari uku da ta kudiri aniyar aiwatar da ginin ofishinta na shiyya da cibiyar horarwa a Minna, gwamnatin jihar Neja za ta samar da naira miliyan dari da hamsin wanda kashi hamsin cikin dari na kudaden da ake bukata domin gudanar da irin wannan aiki.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A sakon sa na fatan alheri, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal wanda ya samu wakilcin kwamishinan kudi na jihar, Mohammed Bello Auta ya sanar da bayar da gudummawar naira miliyan biyar ga taron.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban Cibiyar Kula da Akantoci na Najeriya, DR Haruna Yahaya ya bayyana cewa, cibiyar idan aka kammala da fatan a cikin watan Disamba na wannan shekara za ta sanya wa Gwamnan Jihar Neja suna Umar Bago ICAN Centre.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daga cikin hazikan malaman da suka gabatar da kasidu a wajen bude taron na kwanaki uku na kungiyar ICAN, akwai tsohon mataimakin shugaban jami\u2019ar jihar Kaduna, Farfesa Tanko Mohammed yayin da wakilin Corp Marshal kuma shugaban hukumar kiyaye hadurra ta tarayya, Shehu Mohammed ya gabatar da sakon fatan alheri a wajen taron.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>ALIYU LAWAL.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta samar da tsarin wayarda kan jama\u2019a game da Tattalin Arziki wanda zai inganta gaskiya, kishin \u0199asa, rikon amana da a duk wani abu na rayuwar \u0199asa. &nbsp; Ministan yada labarai da wayar da kan jama\u2019a na kasa, Mohammed Idris ya bayyana haka a wajen bude taron Akanta na shiyyar Arewa na Minna [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6333,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11],"tags":[1119,488],"class_list":["post-6331","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","tag-mina","tag-minista"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/d27ad001-00b5-444b-bf33-0bcbbaa7a2a6.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6331","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6331"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6331\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6334,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6331\/revisions\/6334"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6333"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6331"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6331"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6331"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}