{"id":6322,"date":"2025-09-10T09:55:12","date_gmt":"2025-09-10T09:55:12","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6322"},"modified":"2025-09-10T09:59:53","modified_gmt":"2025-09-10T09:59:53","slug":"birtaniya-ta-ware-fam-miliyan-19-domin-karfafa-gina-makarantu-da-cibiyoyin-lafiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/birtaniya-ta-ware-fam-miliyan-19-domin-karfafa-gina-makarantu-da-cibiyoyin-lafiya\/","title":{"rendered":"Birtaniya Ta Ware Fam Miliyan 19\u00a0 Domin Karfafa Gina Makarantu da Cibiyoyin Lafiya A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Birtaniya, ta hannun ofishin kula da kasashen renon Ingila<strong>\u00a0(FCDO)<\/strong> tare da ha\u0257in gwiwar UNICEF, ta ware Fam Miliyan 19\u00a0 domin \u0199arfafa gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu jure sauyin yanayi a Najeriya.<\/p>\n<p>A \u0199ar\u0199ashin shirin samar da abubuwan dake jure yanayi na fari (CRIBS), Jihar Kano ta amfana da gyaran makarantu da asibitoci guda 55.<\/p>\n<p>Wannan tallafi ya ha\u0257a da sabunta makarantu 28 da cibiyoyin kiwon lafiya na farko guda 27, cikin ha\u0257in gwiwa da gwamnatin Jihar Kano.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6323\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0025-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0025-300x169.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0025-768x432.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0025.jpg 1000w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Yayin bikin \u0199addamar da makarantar firamare ta Wangara a \u0199aramar hukumar Gezawa, wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana cewa gyare-gyaren sun ha\u0257a da hanyoyin zamani masu dacewa da sauyin yanayi, irin su ginin da ke da \u0199arfin jure ambaliya, da kuma amfani da hasken rana don samar da wutar lantarki.<\/p>\n<p>Ta kuma bayyana cewa gyaran zai ba mata damar haihuwa cikin aminci, tabbatar da samun magani cikin lokaci ga yara, da kuma bai wa matasa damar ci gaba da karatu ba tare da katsewa ba.<\/p>\n<p>Daraktar ofishin jakadancin Birtaniya a Abuja, Cynthia Rowe, wacce babbar mai ba da shawara kan ilimi na FCDO, Joseph Wales ya wakilta, ta bayyana cewa shirin CRIBS ya tabbata ne ta hanyar ha\u0257in gwiwa da UNICEF, da Gwamnatin Tarayya, da\u00a0 Bankin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Sextant Foundation, JigSaw, Fab Inc, Crown Agents.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6324\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026-1024x768.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026-1536x1152.jpg 1536w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0026.jpg 1600w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>\u201c<em>Shirin CRIBS na nuni da yadda gine-ginen da ke jure sauyin yanayi za su iya inganta samun kulawa ga al\u2019ummomi masu rauni. Muna fatan wannan tsari zai \u0199ara samun amfani a fa\u0257in Najeriya<\/em>,\u201d in ji ta.<\/p>\n<p>Haka kuma, UNICEF tare da ha\u0257in gwiwar Gwamnatin Jihar Kano, Gwamnatin Kanada, da IHS Towers Nigeria, sun \u0199addamar da na\u2019urar samar da iskar numfashi ta oxygen a asibitin Kwararru na Muhammadu Buhari\u00a0 da ke Karamar Hukumar Nassarawa ta Jihar Kano.<\/p>\n<p>Tun da farko, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan ilimi Dr Ali Haruna Makoda ya wakilta, ya bayyana wannan aikin a matsayin\u00a0 sauyi mai alfanu ga rayuwar al\u2019umma.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa \u0199addamar da makarantar firamare ta Wangara da kuma kaddamar da na\u2019urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a jihar, sun zama ginshi\u0199i wajen samar da iskar da za ta ceci rayuka, musamman na yara da mata masu juna biyu.<\/p>\n<p>Gwamna Yusuf ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin jihar wajen karewa da kula da wadannan wurare domin cimma burin da aka sa gaba.<\/p>\n<p>Abubuwan da suka fi jan hankali a taron sun ha\u0257a da \u0199addamar da makarantar firamare ta Wangara, cibiyar kiwon lafiya ta Gofaro a Gezawa, kaddamar da na\u2019urar samar da iskar oxygen ta farko da ke amfani da hasken rana a asibitin Muhammadu Buhari Specialist Hospital, Nassarawa LGA, da kuma ziyarar ban girma ga Gwamnatin Jihar Kano.<\/p>\n<p><strong>Daga Khadijah Aliyu<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Birtaniya, ta hannun ofishin kula da kasashen renon Ingila\u00a0(FCDO) tare da ha\u0257in gwiwar UNICEF, ta ware Fam Miliyan 19\u00a0 domin \u0199arfafa gina makarantu da cibiyoyin lafiya masu jure sauyin yanayi a Najeriya. A \u0199ar\u0199ashin shirin samar da abubuwan dake jure yanayi na fari (CRIBS), Jihar Kano ta amfana da gyaran makarantu da asibitoci guda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6325,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,4],"tags":[438,1527,39,704],"class_list":["post-6322","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-birtaniya","tag-cribs","tag-kano","tag-unicef"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250910-WA0027.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6322","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6322"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6322\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6332,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6322\/revisions\/6332"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6325"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6322"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6322"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6322"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}