{"id":6309,"date":"2025-09-09T22:34:57","date_gmt":"2025-09-09T22:34:57","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6309"},"modified":"2025-09-10T22:32:25","modified_gmt":"2025-09-10T22:32:25","slug":"birtaniya-ta-ba-da-tallafin-fam-miliyan-19-don-kare-sauyin-yanayi-a-najeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/birtaniya-ta-ba-da-tallafin-fam-miliyan-19-don-kare-sauyin-yanayi-a-najeriya\/","title":{"rendered":"Birtaniya Ta Ba Da Tallafin Fam Miliyan 19 Don Kare Sauyin Yanayi A Najeriya"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Birtaniya ta sanar da bayar da tallafin fam miliyan 19 domin gina asibitoci da makarantun zamani masu jure sauyin yanayi a Najeriya.<\/p>\n<p>Sanarwar ta fito ne a wajen kaddamar da hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Birtaniya, da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da Ma\u2019aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma gwamnatocin jihohin Kano da Jigawa, inda aka kaddamar da makarantu da cibiyoyin lafiya guda 84 da aka gina \u0199ar\u0199ashin shirin <strong>Climate Resilient Infrastructure for Basic Services (CRIBS).<\/strong><\/p>\n<p>CRIBS wani shiri ne na kirkire-kirkire da nuni da sabon salo da zai kare muhimman ayyukan lafiya da ilimi daga barazanar sauyin yanayi.<\/p>\n<p>Najeriya tana matsayi na biyu a duniya wajen fuskantar barazanar sauyin yanayi ga yara, inda miliyoyi ke fuskantar ambaliya, fari, da tsananin zafi a kowace shekara.<\/p>\n<p>Daraktar shirin a Najeriya, Cynthia Rowe, ta bayyana cewa an tsara tsarin CRIBS ne domin tantancewa da \u0199arfafa cibiyoyi 84 , da suka hada da cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 39 da makarantu 45 a Kano da Jigawa, ta hanyar amfani da matakan da suka dace na kariya daga sauyin yanayi.<\/p>\n<p>Ta ce kaddamar da wa\u0257annan cibiyoyin wata babbar nasara ce da ke nuna hanyoyin magance barazanar sauyin yanayi.<\/p>\n<p>A cewarta, Gwamnatin Birtaniya tana alfahari da tallafawa Gwamnatin Najeriya ta wannan tallafin na Miliyan 19 ga shirin CRIBS.<\/p>\n<p>Cynthia Rowe ta \u0199ara da cewa, an yi wannan aiki ne ta hanyar ha\u0257in gwiwar kungiyoyi da kwararru da suka ha\u0257a da: Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Gwamnatin Birtaniya, UNICEF, Bankin Duniya, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Sextant Foundation, JigSaw, Fab Inc, Crown Agent da shirin UK Lafiya.<\/p>\n<p>\u201c<em>CRIBS ya nuna yadda gine-ginen da suka dace da sauyin yanayi za su iya inganta samun ayyukan yau da kullum ga al\u2019ummomin da ke da rauni. Muna fatan wannan hakan zai zama abin koyi da za a yada a fadin Najeriya.\u00a0<\/em><\/p>\n<p>Cynthia ta \u0199ara da cewa wannan kaddamarwar ta yi daidai da manufofin \u0199asa da na jihohi a fannin sauyin yanayi, lafiya da ilimi, sannan tana nuna \u0199udirin Gwamnatin Birtaniya na tallafawa Najeriya wajen rage barazanar sauyin yanayi da inganta ayyukan yau da kullum.<\/p>\n<p>\u201c<em>Wannan \u0199addamarwa shaida ce ga abin da ha\u0257in zai iya cimmawa<\/em>,\u201d in ji wakiliyar UNICEF a Najeriya Wafaa Saeed.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Birtaniya ta sanar da bayar da tallafin fam miliyan 19 domin gina asibitoci da makarantun zamani masu jure sauyin yanayi a Najeriya. Sanarwar ta fito ne a wajen kaddamar da hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Birtaniya, da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, da Ma\u2019aikatar Lafiya ta Tarayya da kuma gwamnatocin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6311,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,4],"tags":[438,1527,120,59],"class_list":["post-6309","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-birtaniya","tag-cribs","tag-gwamnatin-tarayya","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250909-WA0023.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6309","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6309"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6309\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6316,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6309\/revisions\/6316"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6311"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6309"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6309"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6309"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}