{"id":6306,"date":"2025-09-09T22:03:38","date_gmt":"2025-09-09T22:03:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6306"},"modified":"2025-09-09T22:03:38","modified_gmt":"2025-09-09T22:03:38","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-sha-alwashin-horas-da-yara-sanaoi-tun-daga-matakin-firamare","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-sha-alwashin-horas-da-yara-sanaoi-tun-daga-matakin-firamare\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Sha Alwashin Horas Da Yara Sana&#8217;o&#8217;i Tun Daga Matakin Firamare"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar samar da tsari na \u0199asa kan ha\u0253aka sana&#8217;o&#8217;in hannu daban daban.<\/p>\n<p>An bayyana hakan ne a taron Cibiyar Horas da Sana&#8217;o&#8217;i ta Kasa da aka gudanar a Abuja \u0199ar\u0199ashin jagorancin Mataimakin Shugaban \u0198asa, Kashim Shettima, tare da Ministan Ilimi a matsayin mataimakinsa.<\/p>\n<p>Bayan kammala taron, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa tattaunawar ta haifar da \u018aa mai ido, inda ya ce za a aika da kudirin kafa Cibiyar Horas da Sana&#8217;o&#8217;i ta \u0198asa\u00a0 zuwa majalisar dokoki nan ba da da\u0257ewa ba.<\/p>\n<p>Ya ce: <em>\u201cManufar ita ce a daidaita ayyukan dukkan manyan masu ruwa da tsaki a wannan fanni. Kaduna ta riga ta amfana \u0199warai, inda Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da cibiyoyin koyon sana\u2019o\u2019i, inda\u00a0 dalibai sama 32,000 ke koyon sana\u2019o\u2019i daban daban.<\/em><\/p>\n<p>Ministan Ilimi, Farfesa Tunji Alausa, ya jaddada cewa horar da sana\u2019o\u2019in hannu na kan gaba a cikin ajandar\u00a0 gwamnati, wacce ke daidai da al\u0199awarin Shugaba Tinubu na samar da damar ci gaba ga matasan Najeriya.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa sabuwar manhajar \u0199asa yanzu ta mai da hankali ne sosai kan fannoni na musamman guda shida, da suka hada da \u0257inki, kiwon dabbobi, gyaran kwamfuta da wayoyin hannu, da sauransu, wa\u0257anda su ne sana\u2019o\u2019in da kasa ke matukar bukata a yanzu.<\/p>\n<p>Ita kuwa Minista a Ma\u2019aikar\u00a0 Kwadago da Samar da Ayyuka, Nkeiruka Onyejeocha, ta bayyana cewa Majalisar\u00a0 Zartaswa na kokarin tabbatar da cewa yara na samun horo kan sana\u2019o\u2019in hannu tun daga matakin farko na ilimi har zuwa girmansu.<\/p>\n<p>Ta ce <em>\u201cManufar ita ce a tabbatar kowanne yaro ya girma da wata kwarewa, don rage tarin matasan da ba su da aiki. Haku kuma kowa zai samu damar taka muhimmiyar rawa a cikin al\u2019umma.\u201d<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong>Bello Wakili<\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyarta na magance matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ta hanyar samar da tsari na \u0199asa kan ha\u0253aka sana&#8217;o&#8217;in hannu daban daban. An bayyana hakan ne a taron Cibiyar Horas da Sana&#8217;o&#8217;i ta Kasa da aka gudanar a Abuja \u0199ar\u0199ashin jagorancin Mataimakin Shugaban \u0198asa, Kashim Shettima, tare da Ministan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6307,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[120,237],"class_list":["post-6306","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-gwamnatin-tarayya","tag-sanaoi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/VP-Shettima.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6306","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6306"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6306\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6308,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6306\/revisions\/6308"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6307"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6306"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6306"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6306"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}