{"id":629,"date":"2024-03-25T10:37:05","date_gmt":"2024-03-25T10:37:05","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=629"},"modified":"2024-03-25T10:37:05","modified_gmt":"2024-03-25T10:37:05","slug":"zaben-senegal-jamiyyar-adawa-ce-ke-kan-gaba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/zaben-senegal-jamiyyar-adawa-ce-ke-kan-gaba\/","title":{"rendered":"Zaben Senegal : Jami&#8217;yyar Adawa Ce Ke Kan Gaba"},"content":{"rendered":"<p>Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Senegal na nuna dan takarar jam&#8217;iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ne ke kan gaba, lamarinn da ya sanya magoya bayansa fita kan tituna don fara nuna murnar nasara a zaben, ko da yake babban abokin hamayyarsa na jam&#8217;iyyar da ke mulki ya ce sai an gudanar da zaben zagaye na biyu ne za a iya tantance wanda yayi nasara.<\/p>\n<p>Tuni dai akalla \u2018yan takara 5 daga ciki 19 da ke fafatawa a zaben, suka fidda sanarwar taya Faye murna, duk da ya ke tsohon firai ministan kasar Amadou Ba da ke takara a jam\u2019iyar da ke mulki ya ce ya yi wuri mutane su fara murnar sakamakon farko na zaben.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Miliyoyin mutane ne dai suka kada kuri\u2019ar zaben shugaban Senegal na biyar a tarihi, don zabo wanda zai maye gurbin Shugaba Macky Sall da gwamnatinsa ta sha suka kan rashin samar da tsarin saukaka matsin tattalin arziki.<\/p>\n<p>A cewar kafar talabijin din kasar, kashi 71 na yawan masu kada kuri\u2019a miliyan 7 da dubu dari 3 ne suka yi zabe a kasar da ke da akalla yawan mutane miliyan 18.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sakamakon farko na zaben da aka bayyana a gidan talabijin din kasar ya nuna cewa Faye ne ke kan gaba, lamarin da ya sa magoya bayansa fara gudanar da bukukuwa a titunan Dakar babban birnin kasar.<\/p>\n<p>Kawo yanzu dai ba a tan-tance yawan adadin sakamakon rumfunan zabe nawa ne aka kirga ba, daga cikin dubu 15 da dari 633.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A gobe Talata ce ake sa ran fidda sakamakon zaben da dan takara ke bukatar lashe kashi 50 na yawan kuri\u2019un da aka kada kafin yin nasara, ko kuma a je zagaye na biyu.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Sakamakon farko na zaben shugaban kasar Senegal na nuna dan takarar jam&#8217;iyyar adawa Bassirou Diomaye Faye ne ke kan gaba, lamarinn da ya sanya magoya bayansa fita kan tituna don fara nuna murnar nasara a zaben, ko da yake babban abokin hamayyarsa na jam&#8217;iyyar da ke mulki ya ce sai an gudanar da zaben zagaye [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":632,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12,2],"tags":[193,161],"class_list":["post-629","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","category-siyasa","tag-senegal","tag-zaben-shugaban-kasa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/image_2024-03-25_090013585.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/629","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=629"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/629\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":633,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/629\/revisions\/633"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/632"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=629"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=629"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=629"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}