{"id":6288,"date":"2025-09-06T16:54:35","date_gmt":"2025-09-06T16:54:35","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6288"},"modified":"2025-09-06T16:54:35","modified_gmt":"2025-09-06T16:54:35","slug":"rundunar-yan-sanda-ta-nemi-hadin-kan-yan-jarida-a-jigawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/rundunar-yan-sanda-ta-nemi-hadin-kan-yan-jarida-a-jigawa\/","title":{"rendered":"Rundunar &#8216;Yan Sanda Ta Nemi Hadin Kan &#8216;Yan Jarida A Jigawa"},"content":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019Yan Sanda a Jihar Jigawa ta nemi goyon bayan kafafen yada labarai wajen tsara dabarun yaki da laifuka da kuma matsalar shan miyagun kwayoyi a Jihar Jigawa.<\/p>\n<p>Kwamishinan \u2019yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad ne ya yi wannan kira lokacin da mambobin Kungiyar \u2019Yan Jarida bangaren masu ruwaito labarai a Jigawa suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Dutse, babban birnin jihar.<\/p>\n<p>A cewarsa, kafafen yada labarai na taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al\u2019umma kan harkokin tsaro, tare da fadakar jama\u2019a kan gudunmawar da za su iya bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, baya ga bada rahotannin ayyukan \u2019yan sanda, kafafen yada labarai na kara gina kwarin gwiwar jama\u2019a ga hukumomin tsaro, wanda hakan ke sa mutane kara sakin jiki don bayar da muhimman bayanai da za su taimaka wajen dakile aikata lailaifuka da gudanar da bincike.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6289\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0011-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0011-300x169.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0011-1024x576.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0011-768x432.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0011.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Kwamishinan, wanda aka turo shi kwanan nan zuwa jihar, ya ce zai yi amfani da wani sabon salo wanda zai fi mayar da hankali kan hada kai da al\u2019umma, tare da kirkiro da yanayin da kowa zai bada tasa gudunmawar, musamman a lamuran da suka shafi tsaron rayuka da dukiyoyin jama\u2019a.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, \u2019yan sanda za su fadada dangantaka da al\u2019umma maimakon harkar tsaro kadai, domin kara gina amintaka da juna.<\/p>\n<p>CP Muhammad ya ce daga cikin matakan da za su dauka sun hada da tabbatar da kwarin gwiwa a tsakanin jama\u2019a, gudanar da bincike da gurfanar da laifuka da gaggawa domin adalci, da kuma karfafa aikin \u2019yan sanda tare da al\u2019umma.<\/p>\n<p>A nasa jawabin shugaban kungiyar \u2019yan jaridar, Kwamared Muhammad Zangina Kura, ya ce sun kai ziyarar ce domin karfafa dangantaka tsakaninsu da rundunar \u2019yan sanda.<\/p>\n<p>Ya ce, tun shekaru da dama akwai kyakkyawar alaka tsakanin \u2019yan jarida da rundunar a Jigawa, kuma suna da niyyar kara habaka wannan alaka da sabon kwamishina.<\/p>\n<p>Kwamared Kura ya jaddada cewa tsaro nauyi ne na kowa da kowa. Ya kuma tabbatar wa kwamishinan da cewa kungiyar \u2019yan jarida za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da rundunar wajen aiwatar da sabuwar dabarar da ta yi daidai da manufofin Sufeton \u2019Yan Sanda na kasa, Kayode Adeolu Egbetokun, na tabbatar da hada kai wajen yaki da laifuka da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar \u2019Yan Sanda a Jihar Jigawa ta nemi goyon bayan kafafen yada labarai wajen tsara dabarun yaki da laifuka da kuma matsalar shan miyagun kwayoyi a Jihar Jigawa. Kwamishinan \u2019yan sanda na jihar, Dahiru Muhammad ne ya yi wannan kira lokacin da mambobin Kungiyar \u2019Yan Jarida bangaren masu ruwaito labarai a Jigawa suka kai masa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6290,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1246,176,59],"class_list":["post-6288","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-yan-jarida","tag-yan-sanda","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250906-WA0012.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6288","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6288"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6288\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6291,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6288\/revisions\/6291"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6290"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6288"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6288"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6288"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}