{"id":6265,"date":"2025-09-03T17:09:49","date_gmt":"2025-09-03T17:09:49","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6265"},"modified":"2025-09-03T17:09:49","modified_gmt":"2025-09-03T17:09:49","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-bukaci-frsc-ta-kara-kaimi-wajen-kiyaye-hadurra-a-tituna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-bukaci-frsc-ta-kara-kaimi-wajen-kiyaye-hadurra-a-tituna\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci FRSC Ta Kara Kaimi Wajen Kiyaye Hadurra A Tituna"},"content":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da sauran masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen aiwatar da Tsarin Kiyaye Hanyoyi, yana mai jaddada cewa alkaluman hatsarorin mota da ake samu har yanzu suna nuna cewa kasar na fuskantar manyan kalubale.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron shekara-shekara na FRSC karo na takwas a Abuja, Shettima ya ce kiyaye lafiyar hanyoyi aiki ne na hadin gwiwa wanda ke bukatar hadin kan gwamnatin tarayya, jihohi, kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin fararen hula.<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kuduri aniyar kara karfafa tsaro a hanyoyin fadin kasar nan, tare da yabawa FRSC bisa ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin shekaru 37 da suka wuce.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya\u00a0 Sanata George Akume, ya bayyana cewa tsaron hanya muhimmin ginshiki ne na ci gaban kasa, inda ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafawa FRSC ta hanyar horaswa da hadin kai da sauran hukumomi.<\/p>\n<p>Taron ya kuma samu halartar abokan hul\u0257a na \u0199asa da \u0199asa ciki har da FIA Foundation wadda ta yaba da rawar da FRSC ke takawa a fagen kula da hanyoyi.<\/p>\n<p>Masu ruwa da tsaki daga kotuna, jami\u2019an tsaro, jami\u2019o\u2019i da sashen sufuri sun yi alkawarin hada kai wajen magance matsalolin Najeriya musamman yawan mace-macen da ke faruwa sanadiyyar hadurra.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya bukaci Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da sauran masu ruwa da tsaki da su kara kaimi wajen aiwatar da Tsarin Kiyaye Hanyoyi, yana mai jaddada cewa alkaluman hatsarorin mota da ake samu har yanzu suna nuna cewa kasar na fuskantar manyan kalubale. Da yake jawabi a wajen taron [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6266,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1325,120,1523],"class_list":["post-6265","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-frsc","tag-gwamnatin-tarayya","tag-hadurra"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/536290113_1200094845483165_4903376482691547528_n_0a34016823.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6265","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6265"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6265\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6267,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6265\/revisions\/6267"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6266"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6265"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6265"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6265"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}