{"id":6248,"date":"2025-09-03T11:55:52","date_gmt":"2025-09-03T11:55:52","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6248"},"modified":"2025-09-03T11:55:52","modified_gmt":"2025-09-03T11:55:52","slug":"hisbah-ta-kama-wani-mutum-da-ke-yunkurin-safarar-mata-12-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hisbah-ta-kama-wani-mutum-da-ke-yunkurin-safarar-mata-12-a-kano\/","title":{"rendered":"Hisbah Ta Kama Wani Mutum Da Ke Yunkurin Safarar Mata 12 A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da safarar mutane tare da mata 12 a wata tashar mora da ke kan titin\u00a0 Zaria.<\/p>\n<p>Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne\u00a0 yana yunkurin safarar matan\u00a0 zuwa Legas.<\/p>\n<p>Mataimakin Kwamandan Janar na Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa, inda ya ce jami\u2019an hukumar karkashin jagorancin jami&#8217;in da ke kula da tashoshin mota, Muhammad Bashir ne suka cafke wanda ake zargin, wanda dan asalin jihar Borno ne.<\/p>\n<p>Bincike na farko ya nuna cewa an shirya safarar matan ne zuwa kasashen waje ta hanyar Legas, inda za su bi ta Jamhuriyar Benin da kumGhana, sannan daga bisani a kaisu Saliyo.<\/p>\n<p>Ana zargin wanda aka kama da tsara musu takardun izinin shiga kasar Saudiyya domin neman aikin yi.<\/p>\n<p>A cewar Hisbah, matan sun bayyana yayin bincike cewa kowannensu ta riga ta biya Naira miliyan \u0257aya da rabi (\u20a61.5m) a matsayin kafin alkalami, tare da yarjejeniyar cewa za su biya sauran kudin bayan sun samu ayyukan yi a \u0199asar da za a kaisu.<\/p>\n<p>Hukumar ta nuna damuwa cewa irin wannan kudi mai yawa na iya zama jari domin dogaro da kai a gida.<\/p>\n<p>Aminuddeen ya ce matan sun bambanta a shekaru, ciki har da wadda ta kai shekara 50, wasu biyu \u2019yan shekara 23, wasu biyu kuma \u2019yan shekara 20, yayin da sauran mafi yawan su \u2019yan shekara 15 ne kacal. Sun fito ne daga jihohin Katsina, Kano, Borno, Jigawa da Zamfara.<\/p>\n<p>\u201c<em>Wannan abin takaici ne<\/em>,\u201d in ji shi. \u201c<em>Kudin da suka biya ya isa su fara sana\u2019a mai kyau a jiharsu. Amma suka zabi su sa kansu cikin hadarin irin wannan tafiya<\/em>.\u201d Ya bukaci iyaye da su ja hankalin \u2019yayansu game da irin wa\u0257annan lamurra masu hadari.<\/p>\n<p>Kwamandan ya gargadi cewa ko da sun samu takardar izinin shiga Saudiyya, babu tabbacin aikin da za su yi a can. \u201c<em>Idan kuma an kasa samun visa, za a karkatar da su zuwa Saliyo. Wannan lamari hadari ne kuma abin takaici<\/em>,\u201d In ji shi.<\/p>\n<p>Daga karshe, hukumar Hisbah ta mika wanda ake zargi da matan ga Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Kasa (NAPTIP) domin gudanar da cikakken bincike da daukar matakan da suka dace.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da safarar mutane tare da mata 12 a wata tashar mora da ke kan titin\u00a0 Zaria. Rahotanni sun bayyana cewa mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an kama shi ne\u00a0 yana yunkurin safarar matan\u00a0 zuwa Legas. Mataimakin Kwamandan Janar na Hisbah, Sheikh [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6249,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[122,39,1521],"class_list":["post-6248","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-hisbah","tag-kano","tag-safarar-mutane"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/images-6-696x389-1.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6248","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6248"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6248\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6250,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6248\/revisions\/6250"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6249"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6248"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6248"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6248"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}