{"id":6245,"date":"2025-09-03T10:41:58","date_gmt":"2025-09-03T10:41:58","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6245"},"modified":"2025-09-03T10:41:58","modified_gmt":"2025-09-03T10:41:58","slug":"hukumar-nscdc-ta-kama-masu-satar-kayayyakin-lantarki-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/hukumar-nscdc-ta-kama-masu-satar-kayayyakin-lantarki-a-kano\/","title":{"rendered":"Hukumar  NSCDC Ta Kama Masu Satar Kayayyakin Lantarki A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da lalatawa da kuma satar kayayyakin wutar lantarki a jihar.<\/p>\n<p>Jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ga manema labarai a madadin kwamandan jihar, Shafi\u2019u Abdulmumini.<\/p>\n<p>Ya ce an cafke mutanen ne bayan samun sahihan bayanan sirri daga kungiyar sa-kai ta Hayin Da\u2019e, da ke Hotoro, a \u0199aramar hukumar Tarauni.<\/p>\n<p>Abdullahi ya bayyana cewa an kama mutanen da wayoyin lantarki da aka lalata, wa\u0257anda ake zargin sun cire ne daga wata na\u2019urar tiransifoma da ke yankin.<\/p>\n<p>Akasarin wadanda aka kama mazauna yankin ne da aka yi aika-aikar, wadanda\u00a0 shekarunsu suka kama da 18 zuwa 28.<\/p>\n<p>\u201c<em>Bincike na farko ya nuna cewa wa\u0257anda ake zargin sun dade suna addabar mazauna Hayin Da\u2019e, Farawa Kwanar Yashi, da Hotoro, ta hanyar fasa-kwauri, sata, da kuma lalata kayayyakin wutar lantarki<\/em>,\u201d in ji Abdullahi.<\/p>\n<p>Kakakin NSCDC ya ce an riga an samu shaidar furuci daga hannun wa\u0257anda ake zargin, yayin da bincike ke ci gaba domin cafke sauran abokan harkar su.<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike.<\/p>\n<p>Shugaban hukumar, Shafi\u2019u Abdulmumini, ya jaddada aniyar NSCDC wajen kare muhimman kayayyaki da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al\u2019umma a jihar.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bayyana cewa an \u0199ara tsauraran ayyukan sintiri da sa ido a duk fadin Kano domin masu aikata sauran laifuka.<\/p>\n<p>Hukumar ta kuma yaba wa \u2018yan sa-kai bisa bayanan sirri da suka bayar, wanda ya taimaka wajen kama batagarin, tare da kira ga al\u2019umma su ci gaba da kasancewa masu lura da tsaro, da kuma bai wa\u00a0 jami\u2019an tsaro hadin kai domin kawar da aikata laifuka a unguwanninsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>ABDULLAHI JALALUDDEEN<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hedkwatar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) a Jihar Kano ta kama mutane shida da ake zargi da lalatawa da kuma satar kayayyakin wutar lantarki a jihar. Jami\u2019in hul\u0257a da jama\u2019a na hukumar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana hakan ga manema labarai a madadin kwamandan jihar, Shafi\u2019u Abdulmumini. Ya ce an cafke mutanen ne [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6246,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[39,1520,481],"class_list":["post-6245","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-kano","tag-kayan-lantarki","tag-nscdc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250903-WA0013.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6245","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6245"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6245\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6247,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6245\/revisions\/6247"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6246"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6245"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6245"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6245"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}