{"id":6221,"date":"2025-09-01T14:06:38","date_gmt":"2025-09-01T14:06:38","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6221"},"modified":"2025-09-01T14:06:38","modified_gmt":"2025-09-01T14:06:38","slug":"alummar-katsina-sun-koka-kan-yadda-shara-ta-mamaye-titin-ibb","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/alummar-katsina-sun-koka-kan-yadda-shara-ta-mamaye-titin-ibb\/","title":{"rendered":"Al&#8217;ummar Katsina Sun Koka Kan Yadda Shara Ta Mamaye Titin IBB"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left;\">Jama\u2019ar cikin garin Katsina sun nuna damuwa kan yadda shara ta mamaye Titin IBB, hanya mafi cunkoso a cikin garin Katsina, wadda ta tashi daga kan titin Kano zuwa kwaryar jihar, ta kai ga fadar Sarkin Katsina.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Titin IBB na da tarihi a matsayin tsohuwar hanya mafi muhimmanci a garin, wacce ta kunshi muhimman wura da suka hada da sakatariyar tarayya, gidan gwamnatin jihar Katsina, bankuna, kamfanonin inshora, makarantu, hedikwatar jam\u2019iyyun siyasa, ofisoshin kungiyoyi, kamfanonin sayar da motoci, manyan shaguna, da wuraren kasuwanci da dama.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Wani mai shago a wata plaza da ke kan titin, mai suna Abubakar Ali, ya bayyana yadda wuraren zubar da shara a gefen titin suka lalata titin da aka san shi da tsafta a baya.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6223\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0015-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0015-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0015-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0015.jpg 992w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\u201c<em>Muna bukatar a jawo hankalin gwamnati, wannan wuri ya koma wajen zubar da shara. Kwantena na shara sun yi kadan kuma wadanda ke da alhakin kwashewa ba sa yin hakan a kai a kai. Wani lokaci sai bayan watanni suke zuwa su kwashe. Hakan na jawo sauro da wari, suna shafar harkokin kasuwancinmu matuka.\u201d<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Shi ma wani dan kasuwa Salisu Malan, ya bayyana irin wannan damuwa, inda ya ce kusan makonni bakwai ke nan da aka kwashe sharar da ke kusa da shagon, har yanzu ba su sake zuwa ba.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\u201c<em>A da ana kwashe wannan shara a duk ranar Asabar, sannan masu kwashewa sukan share wurin gaba daya. Amma yanzu kwantenan sun lalace saboda sakaci, kuma sun yi kadan. Wannan yanki ya kamata ya samu akalla kwantena biyar amma guda daya ne kawai, kuma duka jama\u2019ar wurin ke amfani da shi. Hakan ya sa kwari sun mamaye wuraren kasuwancinmu<\/em>,\u201d In ji shi.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Ga Hamisu Abdullahi kuwa, babbar matsalar ita ce hadarin lafiya da tarin shara ke haifarwa, ganin yadda ake barinta na makonni ko watanni kafin a dauke.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\u201c<em>Wadannan wurare a da ba wurin zubar da shara ba ne, kwantena ne da ake kwashewa a kowane mako sannan a feshe da magunguna. Amma yanzu ba sa kwashewa, ba sa kuma fesin wuraren. Ba a Titin IBB kadai ba, ko\u2019ina cikin gari haka yake.<\/em><\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-6224\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0011-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0011-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0011-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0011.jpg 992w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\u201c<em>Wannan shara ta kunshi tarkace da dama, ruwan sama na turata cikin magudanan ruwa har cikin gidajen mutane. Hakan babban hadari ne ga lafiyar dan Adam, zai iya haddasa cututtuka da dama. Wani hadari kuma shi ne yadda ake amfani da wuraren zubar da shara wajen yin bayan gida a fili. Ya kamata gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa<\/em>,\u201d In ji Abdullahi.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Wadannan mazauna sun yi kira ga Gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda, da ya dauki mataki ta hanyar umartar hukumomin da abin ya shafa, fa su kara samar da kwantena na shara, da kwandunan gefen hanya da wuraren kona shara a Titin IBB da sauran wuraren cikin garin Katsina.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Haka kuma sun bukaci Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Katsina (SEPA) da ta aiwatar da aikinta yadda ya kamata wajen tabbatar da tsafta da lafiyar muhalli a duk fadin jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\n<p style=\"text-align: left;\"><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\n<p style=\"text-align: left;\">\n<p style=\"text-align: left;\">\n<p style=\"text-align: left;\">\n<p style=\"text-align: left;\">\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Jama\u2019ar cikin garin Katsina sun nuna damuwa kan yadda shara ta mamaye Titin IBB, hanya mafi cunkoso a cikin garin Katsina, wadda ta tashi daga kan titin Kano zuwa kwaryar jihar, ta kai ga fadar Sarkin Katsina. Titin IBB na da tarihi a matsayin tsohuwar hanya mafi muhimmanci a garin, wacce ta kunshi muhimman wura [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6222,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[145,1517],"class_list":["post-6221","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-katsina","tag-titin-ibb-shara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0016.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6221","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6221"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6221\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6225,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6221\/revisions\/6225"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6222"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6221"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6221"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6221"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}