{"id":6218,"date":"2025-09-01T11:44:37","date_gmt":"2025-09-01T11:44:37","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6218"},"modified":"2025-09-01T11:44:37","modified_gmt":"2025-09-01T11:44:37","slug":"gwamnatin-zamfara-ta-jajantawa-iyalan-wadanda-suka-mutu-a-hatsarin-jirgin-ruwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-zamfara-ta-jajantawa-iyalan-wadanda-suka-mutu-a-hatsarin-jirgin-ruwa\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Zamfara Ta Jajantawa Iyalan Wadanda Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana alhininta kan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Juma\u2019a a Nasarawan Kifi, da ke Gundumar Birnin Tudu ta Karamar Hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da ke kokarin tserewa daga harin \u2019yan bindiga.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, Mahmud Muhammad Dantawasa, ya fitar, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa jirgin ruwan ya \u0257auki fasinja ne fiye da \u0199ima, wanda hakan ya jawo kifewar sa a tsakiyar hanya, inda ya\u00a0 haddasa asarar rayuka da dama.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa ana ci gaba da aikin ceto da binciko wadanda suka bace, inda \u0199ungiyoyin gaggawa ke aiki tare da shugabannin al\u2019umma domin tantance adadin mutanen da suka \u0253ace da kuma bayar da agajin gaggawa ga wa\u0257anda suka tsira.<\/p>\n<p>\u201c<em>A madadin Gwamnatin Jihar Zamfara, muna mika ta\u2019aziyyar mu ga iyalan wa\u0257anda suka rasu, tare da ro\u0199on Allah ya jikansu da rahama,<\/em>\u201d In ji sanarwar.<\/p>\n<p>Mahmud Dantawasa ya \u0199ara da cewa gwamnatin jihar na aiki don ganin iyalan da abin ya shafa sun samu tallafi da agaji cikin gaggawa.<\/p>\n<p>A cewarsa, Gwamna Dauda Lawal ya umurci jami\u2019an tsaro da su \u0199ara kaimi wajen gudanar da ayyuka a yankin, domin hana \u0199arin hare-haren \u2019yan bindiga da kuma kare rayukan mazauna \u0199auyukan da abin ya shafa.<\/p>\n<p>Ya sake tabbatar da aniyar gwamnatin Zamfara na kawo \u0199arshen matsalar \u2019yan bindiga.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Daga Aminu Dalhatu<\/strong><\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana alhininta kan mummunan hatsarin jirgin ruwa da ya auku ranar Juma\u2019a a Nasarawan Kifi, da ke Gundumar Birnin Tudu ta Karamar Hukumar Gummi, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane da ke kokarin tserewa daga harin \u2019yan bindiga. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Al\u2019adu na jihar, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6219,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1516,115],"class_list":["post-6218","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hatsarin-ruwa","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/09\/IMG-20250901-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6218","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6218"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6218\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6220,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6218\/revisions\/6220"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6219"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6218"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6218"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6218"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}