{"id":6183,"date":"2025-08-28T19:30:24","date_gmt":"2025-08-28T19:30:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6183"},"modified":"2025-08-28T19:30:24","modified_gmt":"2025-08-28T19:30:24","slug":"arewa-cohesion-ta-kaddamar-da-shuwagabani-na-jihohi-da-kwamitoci-don-inganta-hadin-kai-da-cigaba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/arewa-cohesion-ta-kaddamar-da-shuwagabani-na-jihohi-da-kwamitoci-don-inganta-hadin-kai-da-cigaba\/","title":{"rendered":"Arewa Cohesion Ta Kaddamar da Shuwagabani Na Jihohi Da Kwamitoci Don Inganta Hadin Kai Da Cigaba"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative ta kaddamar da shuwagabanin jihohi da kwamitoci na dindindin domin \u0199arfafa tushen aikin kungiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Daraktan Gidauniyar, Dr. Abdullahi Idris, ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamarwar da aka gudanar a Arewa House, Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamitocin da aka kaddamar sun ha\u0257a da: kwamitin tsare-tsare da dabaru, kwamitin kudi da kwamitin kula da Jama\u2019a, tare da shuwagabanin jihohi na rikon kwarya na kungiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dr. Abdullahi Idris ya bayyana cewa wa\u0257annan sabon tsarin zai taimaka wajen ganin kungiyar ta zauna yanda ya kamata da hangen nesa da zaman lafiya, ha\u0257in kai, da ci gaba mai \u0257aurewa a Arewacin Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma yi bayanin ayyukansu kamar haka, Kwamitin Tsare-tsare da Dabaru zai kula da tsara manufofi, fifita manyan ayyuka, da gano abokan hul\u0257a don tabbatar da cimma manufofin kungiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A kan Kwamitin Kudi kuwa, ya jaddada muhimmancin tara kudade, yin amfani da su cikin hikima, tare da kiyaye gaskiya da lissafi na nagarta.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Dr. Abdullahi Idris ya tabbatar da cewa dorewar kudi da kyakkyawan gudanarwa ne za su tabbatar da nasarar kungiyar nan gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Haka kuma ya jaddada muhimmancin Kwamitin Hula da Jama\u2019a, inda ya bayyana shi a matsayin murya da hoto na kungiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, kwamitin zai inganta sunan kungiyar a idon jama\u2019a, ya ya\u0199i labaran \u0199arya, ya kuma tabbatar da ingantacciyar kafuwa a kafofin yada labarai na gargajiya da na zamani, domin Arewa Cohesion ta zama suna sananne a cikin gida da wajen gida.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Game da matakin \u0199asa kuwa, Daraktan ya haskaka rawar da Kwamishinonin Jihohi za su taka, inda ya ce su ne za su sauke hangen nesa na kungiyar zuwa kowace jiha, \u0199aramar hukuma da kuma gunduma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa aikinsu ya ha\u0257a da tara mambobi, kafa tsare-tsare masu ha\u0257a kowa da kowa, da tabbatar da cewa mata, matasa, tsofaffi da kuma masu nakasa sun samu wakilci a kowane reshe na jihohi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa nadin kwamishinonin jihohi zai \u0257auki watanni 12 a matsayin gwaji, daga bisani kuma nagarta da sadaukarwa za su tantance sahihancin mukamansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Yayin kaddamar da kwamitoci da kwamishinonin, Dr. Idris ya tunatar da su cewa an za\u0253e su ne bisa \u0199warewa, gaskiya da sadaukarwa, ba saboda sa\u2019a ba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya shawarce su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, tawali\u2019u da ladabi, yana mai jaddada cewa nasarar kungiyar ta dogara da yadda za su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>COV: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Kungiyar Arewa Cohesion for Peace, Unity and Development Initiative ta kaddamar da shuwagabanin jihohi da kwamitoci na dindindin domin \u0199arfafa tushen aikin kungiyar. &nbsp; Daraktan Gidauniyar, Dr. Abdullahi Idris, ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamarwar da aka gudanar a Arewa House, Kaduna. &nbsp; Kwamitocin da aka kaddamar sun ha\u0257a da: kwamitin tsare-tsare [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":6184,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[639,301,1506,1510,1508,1333,1509,1507],"class_list":["post-6183","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-arewa","tag-cigaba","tag-cohesion","tag-hadin-kai","tag-jihohi","tag-kaddamar","tag-kwamitoci","tag-shuwagabani"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250828-WA0026.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6183","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6183"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6183\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6185,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6183\/revisions\/6185"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6184"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6183"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6183"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6183"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}