{"id":6174,"date":"2025-08-28T16:43:06","date_gmt":"2025-08-28T16:43:06","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6174"},"modified":"2025-08-28T16:43:06","modified_gmt":"2025-08-28T16:43:06","slug":"gwamna-dauda-lawal-ya-amince-da-sabbin-nade-nade-a-jihar-zamfara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-dauda-lawal-ya-amince-da-sabbin-nade-nade-a-jihar-zamfara\/","title":{"rendered":"Gwamna Dauda Lawal Ya Amince Da Sabbin Nade-nade a Jihar Zamfara"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin sabbin jami\u2019ai da suka hada da Manyan Mataimaka na Musamman, da Mambobin Kwamitoci, da Shugabannin Hukumomi da Ma\u2019aikatun Gwamnati, domin \u0199arfafa shugabanci da inganta gudanar da ayyuka a jihar.<\/p>\n<p>Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakin sa na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Sulaiman Ahmad Tudu, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa nade-naden sun fara aiki nan take.<\/p>\n<p>A cewar sanarwar, an nada Aliyu Adamu Tsafe a matsayin Shugaban Hukumar kafafen sadarwa ta Zamfara, yayin da mambobin suka ha\u0257a da Rufai Muhammad Anka, da Hassana Muhammad Bukkuyum, da Muhammad Tanko Khalil, da Yahaya Buhari Bungudu, da Adamu Sani Katuru, da kuma Idris Baba Shinkafi.<\/p>\n<p>Haka kuma Kwamitin ya \u0199unshi Kwamishinonin Ma\u2019aikatun\u00a0 yada labarai, da na Shari\u2019a, da na ma&#8217;aikatar Ku\u0257i, da na Harkokin \u0198ananan Hukumomi, da na ma&#8217;aikatar Kasuwanci, da na Harkokin Addini, sai Shugabar Hukumar Haraji ta Jihar, tare da Daraktan Hukumar Yada Labarai wanda zai kasance a matsayin Sakataren kwamitin.<\/p>\n<p>Domin tabbatar da wakilci a fannoni daban-daban na siyasa a fa\u0257in jihar, Gwamna Lawal ya amince da nadin Manyan Mataimaka na Musamman kan Harkokin Siyasa daga kowace mazabar Sanata guda uku, da suka hada da Nura Abdullahi Tsafe, da\u00a0 Aminu Salmanu Shinkafi, da Nasiru Rabiu.<\/p>\n<p>Haka kuma, Aisha Jamilu Dinawa ta samu mukamin Mataimakiyar Musamman kan Harkokin Yada Labarai, an kuma nada Salisu Isah a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tallafawa Marasa \u0198arfi, yayin da aka nada Hassan Muhammad a matsayin Babban Sakataren Hukumar Wasanni ta Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>Bugu da \u0199ari, an nada Bilkisu Sani Makaranta a matsayin Sakatariyar Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>A wani bangare, Gwamna Lawal ya amince da sauya wurin aiki ga Amina Mustapha Ismail daga Hukumar Tsare-tsaren Finafinai ta Jihar zuwa Kamfanin Zuba Jari da Cigaban Kadarori na Zamfara a matsayin Babbar Darakta, an kuma umurce ta da ta mika ragamar hukumar ga babban darakta mafi girma kafin ta koma ga sabon mukaminta.<\/p>\n<p>Gwamna Dauda Lawal ya taya wadanda aka nada murna, tare da yin kira gare\u00a0 su da su\u00a0 gudanar da ayyukansu bgaskiya da jajircewa, bisa ga tsarin ceto jihar da gwamnatin sa ta \u0257auka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da nadin sabbin jami\u2019ai da suka hada da Manyan Mataimaka na Musamman, da Mambobin Kwamitoci, da Shugabannin Hukumomi da Ma\u2019aikatun Gwamnati, domin \u0199arfafa shugabanci da inganta gudanar da ayyuka a jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da Mataimakin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6177,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1039,115],"class_list":["post-6174","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-nade-nade","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250828-WA0016.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6174","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6174"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6174\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6178,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6174\/revisions\/6178"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6177"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6174"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6174"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6174"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}