{"id":6163,"date":"2025-08-27T20:27:42","date_gmt":"2025-08-27T20:27:42","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6163"},"modified":"2025-08-27T20:32:08","modified_gmt":"2025-08-27T20:32:08","slug":"cikar-jigawa-shukaru-34-gwamna-namadi-ya-yabawa-tsoffin-shugabanni","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/cikar-jigawa-shukaru-34-gwamna-namadi-ya-yabawa-tsoffin-shugabanni\/","title":{"rendered":"Cikar Jigawa Shekaru 34: Gwamna Namadi Ya Yabawa Tsoffin Shugabanni"},"content":{"rendered":"<p>Gwamna Malam Umar Namadi ya yaba wa shugabannin da suka gabata bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi wajen shimfi\u0257a tubalin ci gaban jihar tun daga shekarar 1991 zuwa yau.<\/p>\n<p>A taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, gwamnan ya ce bikin cika shekaru 34 da kafuwar jihar dama ce ta tunawa, tare da murna da kuma sabunta aniyar ci gaban Jigawa.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa jihar ta samu sauyi a fannoni da dama ciki har da noma, ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da ci gaban zamantakewa. A cewarsa, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokari kan wa\u0257annan nasarori tare da bullo da sabbin hanyoyi na bun\u0199asa jihar.<\/p>\n<p>Namadi ya jaddada kudurinsa na aiwatar da manufofin gwamnatinsa 12, wadanda suka ha\u0257a da samar da ayyukan yi, ha\u0253aka noma, inganta kiwon lafiya da ilimi, da kuma raya ababen more rayuwa.<\/p>\n<p>Ya ce gwamnati ta kaddamar da manyan shirye-shirye a fannoni da dama ciki har da injinan noma, ilimi, kiwon lafiya, hanyoyi da kuma tallafa wa matasa, domin inganta hidima da tabbatar da kyakkyawan shugabanci.<\/p>\n<p>Gwamnan ya yi kira ga al\u2019ummar jihar da su ha\u0257a hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jihar, yana mai cewa \u201cCi gaban Jigawa alhaki ne na kowa.\u201d<\/p>\n<p>Ya tabbatar wa jama\u2019a cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da inganta tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da jin\u0199ai, domin rage talauci da inganta rayuwar jama\u2019a.<\/p>\n<p>A \u0199arshe, Gwamna Namadi ya gode wa jama\u2019ar Jigawa bisa goyon bayan da suke ba shi, yana mai al\u0199awarin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai gaskiya da rikon amana akoda yaushe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Malam Umar Namadi ya yaba wa shugabannin da suka gabata bisa jajircewa da sadaukarwar da suka yi wajen shimfi\u0257a tubalin ci gaban jihar tun daga shekarar 1991 zuwa yau. A taron manema labarai da aka gudanar a fadar gwamnatin Dutse, gwamnan ya ce bikin cika shekaru 34 da kafuwar jihar dama ce ta tunawa, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6164,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[59,1505],"class_list":["post-6163","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-jigawa","tag-shekaru-34"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250827-WA0038.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6163","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6163"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6163\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6168,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6163\/revisions\/6168"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6164"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6163"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6163"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6163"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}