{"id":6155,"date":"2025-08-27T14:38:17","date_gmt":"2025-08-27T14:38:17","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6155"},"modified":"2025-08-27T14:38:17","modified_gmt":"2025-08-27T14:38:17","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-tallafa-wa-manoma-352-a-nasarawa-da-kayayyakin-noma-na-zamani","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-tallafa-wa-manoma-352-a-nasarawa-da-kayayyakin-noma-na-zamani\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa Wa Manoma 352 A Nasarawa Da Kayayyakin Noma Na Zamani"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya tare da Asusun Samar da Kudade Domin Bunkasa Harkokin Noma(IFAD) da Shirin Sarrafa Amfanin Gona (VCDP) sun fara raba kayayyakin noman zamani da mashin mai kafa uku\u00a0 ga manoma 352 a Jihar Nasarawa domin kakar noman bana.<\/p>\n<p>Shugabar shirin IFAD-VCDP, Dr. Eunice Adgidzi ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a Lafiya, babban birnin jihar, inda ta ta bayyana cewa shirin ya fi karkata ne ga kanana manoman shinkafa da rogo.<\/p>\n<p>Ta ce shirin wani bangare ne na \u0199o\u0199arin da ake yi na sauya fannin noma zuwa abin da zai kawo wadatar abinci, samar da arziki da kuma ci gaba mai \u0257orewa a Jihar Nasarawa.<\/p>\n<p>Manoma 352 da suka amfana an za\u0253o su ne daga kananan hukumomi biyar da shirin ya shafa a jihar, da suka hada da Lafiya, Nasarawa, Doma, Karu da Wamba.<\/p>\n<p>Kayayyakin da aka raba sun ha\u0257a da buhunan iri shinkafa mai\u00a0 nauyin kilo 9,600, da buhunan 1,408 takin NPK 1,408, da buhuna 384 na takin Urea, da lita 352 na maganin ciyawa mara za\u0253i, da lita 352 na maganin ciyawa mai za\u0253i, da kuma rassa 8,000 na rogo domin dashe.<\/p>\n<p>Haka kuma, an raba mashin mai kafa uku guda tara ga wasu manoma domin sau\u0199a\u0199e musu jigilar kayan gona zuwa kasuwa, wanda hakan zai taimaka wajen rage asarar bayan girbi.<\/p>\n<p>Dr. Adgidzi ta jaddada cewa ha\u0257in gwiwar Gwamnatin Tarayya da IFAD da gwamnatin jihar, na nuna jajircewar samar wa manoma kayan aikin da za su taimaka musu wajen samun nasara.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Kwamishinan Noma na Jihar Nasarawa, Alhaji Umaru Tanko Tunga, ya bayyana cewa wannan shiri zai \u0199ara samar da abinci, rage asarar bayan girbi da kuma inganta rayuwar kananan manoma.<\/p>\n<p>Ya shawarci manoman da suka amfana da su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, sannan ya yaba wa Gwamna Abdullahi Sule bisa samar da yanayin da ya ba da damar nasarar shirye-shiryen noman a jihar.<\/p>\n<p>A martanin su, wasu daga cikin manoman da suka amfana kamar su Lazarus Okwugya daga Assakio, da Joseph Abimiku da Fatima Shuaibu daga unguwar Azuba, sun nuna godiya ga shirin VCDP bisa irin tallafin da ya kawo, wanda suka ce ya inganta yawan amfanin gona da kuma rayuwarsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aliyu Muraki<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya tare da Asusun Samar da Kudade Domin Bunkasa Harkokin Noma(IFAD) da Shirin Sarrafa Amfanin Gona (VCDP) sun fara raba kayayyakin noman zamani da mashin mai kafa uku\u00a0 ga manoma 352 a Jihar Nasarawa domin kakar noman bana. Shugabar shirin IFAD-VCDP, Dr. Eunice Adgidzi ce ta kaddamar da rabon kayayyakin a Lafiya, babban birnin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6157,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10],"tags":[1502,381,348],"class_list":["post-6155","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-ifad-vcdp","tag-manoma","tag-nasarawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Nasarawa-map.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6155","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6155"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6155\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6158,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6155\/revisions\/6158"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6157"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6155"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6155"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6155"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}