{"id":6131,"date":"2025-08-27T08:10:20","date_gmt":"2025-08-27T08:10:20","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6131"},"modified":"2025-08-27T08:10:20","modified_gmt":"2025-08-27T08:10:20","slug":"jamiar-abdulkadir-kure-tana-daya-daga-cikin-jamioin-ci-gaban-kasa-vc","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jamiar-abdulkadir-kure-tana-daya-daga-cikin-jamioin-ci-gaban-kasa-vc\/","title":{"rendered":"Jami&#8217;ar Abdulkadir Kure Tana Daya Daga Cikin Jami&#8217;o&#8217;in Ci gaban Kasa &#8211; VC"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban jami\u2019ar Abdulkadir Kure da ke jihar Neja, Farfesa Mohammed Aliyu Paiko ya bayyana cewa jami\u2019ar na daya daga cikin jami\u2019o\u2019in da ke bunkasa cikin sauri a Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar \u2018yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Neja a ofishinsa da ke Minna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Farfesa Aliyu Paiko ya bayyana cewa jami\u2019ar da ta fara daukar dalibai kusan 100 a shekarar 2024 a yanzu haka tana da dalibai sama da 700 domin a cewarsa karin dalibai suna kan aikin rijistar ne saboda jami\u2019ar tana dada daukaka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban jami\u2019ar ya ci gaba da bayyana cewa, bisa ga manufar fadada jami\u2019ar, sama da dalibai 3,500 ne suka rigaya suka mika takardar neman gurbin karatu na shekarar 2025\/2026 yana mai jaddada cewa jami\u2019ar ta riga ta zama cibiyar kasuwanci a dukkan fannoni musamman a fannin ilimi na musamman.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai ya bayyana cewa ta hanyar Abdulkadir Kure Center for Basic and Professional Studies da GreenTech ICT Hub Initiative, an bude jami\u2019ar ne domin hadin gwiwa da kwararru musamman ma\u2019aikatan yada labarai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A nasa jawabin, shugaban kungiyar \u2018yan jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Abu Nmodu ya bayyana cewa makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa da kungiyoyin biyu ke da shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Kwamared Abu Nmodu wanda ya jaddada rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen fadakarwa, ilmantar da jama\u2019a da kuma nishadantar da jama\u2019a, ya sanar da Shugaban kungiyar cewa NUJ na gudanar da kwasa-kwasan ilimi kan harkokin yada labarai da aikin jarida a karkashin cibiyar \u2018yan jarida ta kasa da kasa (IIJ) a dakin taro na IBB Pen House da ke Minna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban kungiyar ta NUJ ya bada tabbacin Shugaban jami\u2019ar da hukumar gudanarwar jami\u2019ar na ci gaba da bayar da goyon baya domin baiwa kungiyar damar cimma burin da ta sa a gaba.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>ALIYU LAWAL.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban jami\u2019ar Abdulkadir Kure da ke jihar Neja, Farfesa Mohammed Aliyu Paiko ya bayyana cewa jami\u2019ar na daya daga cikin jami\u2019o\u2019in da ke bunkasa cikin sauri a Najeriya. &nbsp; Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar \u2018yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar Neja a ofishinsa da ke Minna. &nbsp; [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":6132,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[1496],"class_list":["post-6131","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kure-minna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/images-1-2.jpeg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6131","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6131"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6131\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6133,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6131\/revisions\/6133"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6132"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6131"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6131"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6131"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}