{"id":6112,"date":"2025-08-25T14:03:50","date_gmt":"2025-08-25T14:03:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6112"},"modified":"2025-08-25T14:03:50","modified_gmt":"2025-08-25T14:03:50","slug":"harin-taaddanci-gwamnatin-katsina-bukacin-hadin-kan-alummar-jihar","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/harin-taaddanci-gwamnatin-katsina-bukacin-hadin-kan-alummar-jihar\/","title":{"rendered":"Harin Ta\u2019addanci: Gwamnatin Katsina Bukacin Hadin Kan Al&#8217;ummar Jihar"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kira ga al\u2019ummomin da ke zaune a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro da su ba da ha\u0257in kai ga jami\u2019an tsaro a ci gaba da ya\u0199i da &#8216;yan ta\u2019addanci da masu garkuwa da mutane.<\/p>\n<p>Mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Faruk Jobe ne ya yi wannan kira bayan taron gaggawa maga da al&#8217;amuran tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar da ke Katsina.<\/p>\n<p>Jobe ya bayyana cewa an kira taron ne domin sake tantance tsarin tsaron jihar da nufin \u0199arfafa ha\u0257in gwiwa mai tasiri tsakanin hukumomin tsaro wajen ya\u0199i da ta\u2019addanci, da yin sintiri a yankuna da kuma musayar bayanai domin tabbatar da nasarar ya\u0199i da \u2018yan bindiga.<\/p>\n<p>Ya ce bisa ga rahotannin baya-bayan nan daga shugabannin hukumomin tsaro daban-daban, jami\u2019an tsaro na iya bakin \u0199o\u0199arinsu, amma ba za a iya samun gagarumar nasara ba, ba tare da tallafi da ha\u0257in kai daga al\u2019ummomi ba.<\/p>\n<p>Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa a fannin kayan aikin soja, Jihar Katsina ce tafi shirye-shirye a shiyyar Arewa maso Yamma, tana da motoci masu sulke 43, kayan sintiri da na ya\u0199i, tare da\u00a0 jajirtattun jami\u2019an Sojojin Najeriya, Rundunar Sama, \u2018Yan sanda, DSS, \u2018yan sa-kai, mafarauta da kuma jami\u2019an tsoro na jihar wato Community Watch Corps.<\/p>\n<p>Yayin da yake bayyana harin da aka kai a Unguwar Mantau da ke Karamar Hukumar Malumfashi a matsayin aikin ta\u2019addanci na rashin imani, Jobe ya yi ta\u2019aziyya ga mutanen yankin tare da tabbatar da cewa za a kamo masu laifin kuma a hukunta su bisa doka.<\/p>\n<p>\u201c<em>Ba za mu huta ba sai mun kawar da ta\u2019addancin \u2018yan bindiga daga jihar nan, sai dai muna bukatar ha\u0257in kai sosai daga al\u2019umma musamman a fannin bayar da bayanai. Dakarunmu ba za su iya aiki su ka\u0257ai ba, suna bu\u0199atar ha\u0257in kai daga al\u2019ummomi.\u201d<\/em><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Katsina ta yi kira ga al\u2019ummomin da ke zaune a yankunan da ake fama da matsalolin tsaro da su ba da ha\u0257in kai ga jami\u2019an tsaro a ci gaba da ya\u0199i da &#8216;yan ta\u2019addanci da masu garkuwa da mutane. Mukaddashin Gwamnan Jihar, Alhaji Faruk Jobe ne ya yi wannan kira bayan taron gaggawa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6113,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1494,145],"class_list":["post-6112","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-harin-taaddanci","tag-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250825-WA0032.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6112","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6112"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6112\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6114,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6112\/revisions\/6114"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6113"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6112"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6112"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6112"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}