{"id":6071,"date":"2025-08-22T17:29:53","date_gmt":"2025-08-22T17:29:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6071"},"modified":"2025-08-22T17:29:53","modified_gmt":"2025-08-22T17:29:53","slug":"an-bukaci-gwamnatin-tarayya-da-na-jihohi-su-kafa-maaikatun-harkokin-iyali","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-bukaci-gwamnatin-tarayya-da-na-jihohi-su-kafa-maaikatun-harkokin-iyali\/","title":{"rendered":"An Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Na Jihohi Su Kafa Ma&#8217;aikatun Harkokin Iyali"},"content":{"rendered":"<p>An yi kira ga Gwamnatin tarayya da na jihohi da su kafa Ma\u2019aikatu na Harkokin Iyali domin magance aikata laifuka da rushewar tarbiyya a \u0199asar nan, wanda ake dangantawa da lalacewar abi\u2019un iyali.<\/p>\n<p>Limamin Masallacin Juma\u2019a na Kofar Marusa da ke Katsina, Sheikh Nura Gwanda, ne ya yi wannan kira a cikin hudubar Juma\u2019ar da ya gabatar mai taken <em>\u201cIyaye da Tarbiyya a Matsayin Amanar Allah\u201d<\/em>.<\/p>\n<p>Ya bayyana wasu daga cikin munanan dabi\u2019u da suka bulla sakamakon rugujewar darajar iyali, da suka ha\u0257a da shan miyagun \u0199wayoyi, ta\u2019addanci, fashi da makami, \u2018yan daba, garkuwa da mutane da kuma rashawa a gwamnati da ma kamfanoni masu zaman kansu.<\/p>\n<p>Sheikh Gwanda ya bayyana cewa mafi yawan \u0199asashen Gabas ta Tsakiya da Turai suna da Ma\u2019aikatu na Harkokin Iyali wa\u0257anda ke kula da al\u2019amurran aure, tarbiyyar yara, gado, cin zarafin iyali, cin zarafin yara, saki, kula da yara bayan rabuwar aure da sauran batutuwan iyali.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa tunda iyali\u00a0 ne tubalin gina al\u2019umma, kafa irin wannan ma\u2019aikata a Najeriya zai taimaka matu\u0199a wajen shawo kan matsaloli irin su cin zarafin yara, zaman kashe wando, tabarbarewar tarbiyya da sauran munanan dabi\u2019u musamman a arewacin \u0199asar.<\/p>\n<p>Liman ya \u0199ara da cewa kafa Ma\u2019aikatar Harkokin Iyali zai kuma magance tushen matsalolin tsaro a \u0199asar nan, duba da cewa mafi yawan masu aikata laifuka yara ne da aka yar da su ko kuma \u2018ya\u2019yan da iyayen su ba sa tare da juna.<\/p>\n<p><strong><em>Daga Isma\u2019il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An yi kira ga Gwamnatin tarayya da na jihohi da su kafa Ma\u2019aikatu na Harkokin Iyali domin magance aikata laifuka da rushewar tarbiyya a \u0199asar nan, wanda ake dangantawa da lalacewar abi\u2019un iyali. Limamin Masallacin Juma\u2019a na Kofar Marusa da ke Katsina, Sheikh Nura Gwanda, ne ya yi wannan kira a cikin hudubar Juma\u2019ar da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6072,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1490,145],"class_list":["post-6071","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-iyali","tag-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250822-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6071","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6071"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6071\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6073,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6071\/revisions\/6073"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6072"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6071"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6071"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6071"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}