{"id":6065,"date":"2025-08-22T12:27:42","date_gmt":"2025-08-22T12:27:42","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6065"},"modified":"2025-08-22T12:27:42","modified_gmt":"2025-08-22T12:27:42","slug":"acf-ta-sha-alwashin-kwaicewa-tsoma-baki-a-harkokin-siyasa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/acf-ta-sha-alwashin-kwaicewa-tsoma-baki-a-harkokin-siyasa\/","title":{"rendered":"ACF Ta Sha Alwashin Kwaicewa Tsoma Baki A Harkokin Siyasa"},"content":{"rendered":"<p>Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta ja hankalin shugabanni da al\u2019ummar Arewacin Najeriya da su kasance masu taka-tsan-tsan da hadin kai a yayin da ake fuskantar matsalolin tsaro, rikicin siyasa da bala\u2019o\u2019in muhalli da ke barazana ga zaman lafiya a yankin.<\/p>\n<p>Shugaban Kungiyar, Cif Mamman Mike Osuman (SAN) ne ya yi wannan kira a ranar Alhamis a Kaduna, yayin taron kwamitin zartarwa na kasa karo na 78, inda ya gargadi shugabannin Arewa su guji sakaci da kuma yarda da labaran kanzon kurege.<\/p>\n<p>\u201c<em>Wannan ba lokacin ne da za mu zauna mu zuba ido ba. Ya zama wajibi mu kasance tsintsiya madaurinki daya wajen fuskantar rashin jituwa, son zuciya, shakku, yaudara, da jita-jita<\/em>\u201d In ji shi.<\/p>\n<p>Ya ce Arewa ta dade tana fama da matsalolin tsaro daga ta\u2019addanci zuwa \u2019yan fashi da kuma bala\u2019o\u2019in da suka shafi muhalli da suka hada da ambaliyar ruwa, da zaizayar kasa, yana mai bayyana cewa ACF na cikin damuwa matuka kan irin asarar rayuka da ake yi.<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma tuna da jerin fitattun shugabannin Arewa da aka rasa kwanan nan ciki har da tsohon Shugaban ACF, Cif Audu Ogbeh; da Sakatare Janar na biyu, Alhaji Umar Moriki, da tsohon Minista, Farfesa Jubril Aminu, da dattijo Alhaji Aminu Dantata, da tsohon Babban Alkalin Najeriya, Mai Shari\u2019a Muhammad Uwais,\u00a0 da kuma tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari.<\/p>\n<p>Ya sake jaddada matsayin ACF na rashin tsoma baki a siyasa, inda ya bayyana cewa ko da yake mambobinta na da hakkin shiga\u00a0 jam\u2019iyyun siyasa daban-daban a matsayinsu na &#8216;yan kasa, amma kungiyar ba za ta taba jingina kanta da wata jam\u2019iyya ba.<\/p>\n<p>\u201c<em>ACF ba ta da jam\u2019iyya, kuma ba za ta taba kasancewa karkashin kowace jam&#8217;iyya ba. Abin da muke da shi kawai shi ne kishin Arewa da jama\u2019arta, cikin mutunta hadin kan Najeriya<\/em>,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-full wp-image-6067\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250822-WA0002.jpg\" alt=\"\" width=\"255\" height=\"198\" \/><\/p>\n<p>Osuman ya ce kungiyar za ta ci gaba da yin aiki tare da kungiyoyi masu irin wannan manufa, inda ya bayyana cewa Forum for National Restoration sun gayyace shi domin gabatar da jawabi a wurin taron su na kasa.<\/p>\n<p>Dangane da shirye-shiryen gaba, ya sanar da cewa ACF na dab da kammala shiri domin bikin cika shekaru 25 da kafuwa, wanda aka tsara za a gudanar daga ranar 15 zuwa 30 ga watan Oktoban 2025.<\/p>\n<p>\u201c<em>An riga an kafa kwamitoci, kuma sun fara aiki. Na halarci wasu tarurrukan nasu, abin da suke yi lalle abin a yaba\u00a0 ne.<\/em><\/p>\n<p>Ya kuma gargadi mambobi su guji yada ra\u2019ayoyi marasa tushe ko masu tsattsauran ra\u2019ayi a dandalin sadarwa na ACF, yana mai cewa ya kamata su rika tuntubar\u00a0 shugabannin jihohi ko kuma sakatariyar kungiyar.<\/p>\n<p>Shugaban ya bayyana cewa ttaronna ACF karo na 78 ya kunshi batutuwa guda 12, ciki har da sabuntawa kan kamfanin ARECON da kuma batun \u201cETTE.\u201d Ya ce kashi na goma na ajandar taro, wato State of the Nation, zai kasance karkashin jagorancin Jami\u2019in Yada Labaran ACF, Farfesa Tukur Baba, wanda daga karshe za a fitar da sanarwa.<\/p>\n<p>A karshe, Osuman ya yi kira ga \u2019yan Arewa da su kasance masu juriya, bin doka da oda da kuma hadin kai, yana mai cewa wannan lokaci ne na da yankin Arewa ke fuskantar kalubale daban daban.<\/p>\n<p>Ya kuma jagoranci addu\u2019ar neman gafara ga shugabanni da \u2019yan Arewa da suka riga mu gidan gaskiya.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar manyan shugabannin Arewa, inda daga bisani suka shiga zaman taron sirri don tattaunawa game da\u00a0 hadin kan al&#8217;ummar yankin Arewa, da\u00a0 kalubalen tsaro da kuma shirin bikin cika shekaru 25 na kungiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Abdullahi Shettima\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta ja hankalin shugabanni da al\u2019ummar Arewacin Najeriya da su kasance masu taka-tsan-tsan da hadin kai a yayin da ake fuskantar matsalolin tsaro, rikicin siyasa da bala\u2019o\u2019in muhalli da ke barazana ga zaman lafiya a yankin. Shugaban Kungiyar, Cif Mamman Mike Osuman (SAN) ne ya yi wannan kira a ranar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6066,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2,8],"tags":[1489,33],"class_list":["post-6065","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","category-tsaro","tag-acf","tag-kaduna"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250822-WA0001.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6065","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6065"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6065\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6068,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6065\/revisions\/6068"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6066"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6065"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6065"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6065"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}