{"id":6020,"date":"2025-08-21T14:32:29","date_gmt":"2025-08-21T14:32:29","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=6020"},"modified":"2025-08-21T14:32:29","modified_gmt":"2025-08-21T14:32:29","slug":"gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-shirin-inganta-rayuwar-matasan-da-suka-tuba-daga-ayyukan-daba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-shirin-inganta-rayuwar-matasan-da-suka-tuba-daga-ayyukan-daba\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Shirin Inganta Rayuwar Matasan Da Suka Tuba Daga Ayyukan Daba"},"content":{"rendered":"<p style=\"text-align: left;\">Gwamnatin Jihar Kano tare da ha\u0257in gwiwar Hukumar \u2019Yan Sanda ta \u0198asa sun kammala binciken\u00a0 matasa 718 da suka daina harkar daba a \u0199ar\u0199ashin shirin &#8216;Safe Corridor Project&#8217; na jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Wannan mataki muhimmin tsari ne na rage rashin tsaro da kuma bai wa matasa masu rauni damar zama nagari.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Bikin \u0199addamar da shirin ya gudana ne a ginin &#8216;yan sanda na officers&#8217; mess da ke Bompai a Kano. A wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin afuwar a matsayin dabarar zaman lafiya wajen magance laifuka da tashin hankali a jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Gwamnan\u00a0 wanda Kwamishinan Ya\u0257a Labarai da Harkokin Cikin Gida, Alhaji Ibrahim Waiya ya wakilta, ya bayyana cewa \u0199arin matasa 960 da suka tuba na jiran tantancewa a mataki na gaba. Yana mai cewa an tsara shirin ne don kawo \u0199arshen matsalolin tada-zaune-tsaye, satar waya da sauran laifuka, ta hanyar bai wa masu tuba damar gyara rayuwarsu don sake dawowa cikin al\u2019umma, da kuma samun taimakon dogaro da kai.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\u201c<em>Mun yi imanin cewa idan muka rungumi wa\u0257annan matasa ta hanyar wannan dabarar zaman lafiya, za mu iya shawo kan \u0199alubalen da muke fuskanta na fadan daba, wanda ya da\u0257e yana damun al\u2019umma. Babban burinmu shi ne mu sa harkar daba ta zama tarihi a Kano.\u201d<\/em> In ji Gwamna Yusuf.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Ya \u0199ara da cewa za a yi wa matasan gwajin miyagun \u0199wayoyi karkashin\u00a0 shirin gyaran dabi&#8217;u na hukumar yaki da tu&#8217;ammali da miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA. &#8220;<em>Wa\u0257anda suka tsallake wannan mataki za su samu tallafi daga gwamnati domin dogaro da kansu, don kauce wa komawa ga aikata laifi&#8221;. In ji shi.<\/em><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">A nasa jawabin, Kwamishinan \u2019Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya yaba da \u0199o\u0199arin gwamnati tare da tabbatar da aniyar hukumar \u2019yan sanda na ci gaba da tallafa wa shirin.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Ya jaddada cewa ya\u0199i da laifuka ba na \u2019yan sanda ba ne ka\u0257ai, ya bukaci iyalai da al\u2019umma su rungumi wannan aiki tare da hukumomin tsaro.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Shi ma Kwamandan NDLEA na Jihar Kano, Malam Abubakar Idris, ya bayyana goyon bayan hukumar ga shirin &#8216;<em>Safe Corridor Project<\/em>&#8216;. Yana mai\u00a0 cewa amfani da miyagun \u0199wayoyi na daya daga cikin abubuwan da ke jefa matasa cikin tashin hankali, ya kuma jaddada muhimmancin ganin gwamnatin ta kara zage dantse domin samun zaman lafiya a jihar.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki da suka halarci taron sun shawarci matasan da su tsaya tsayin daka a kan tubansu, suna gargadin cewa kada su yi asarar wannan dama da gwamnati ta basu.<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">Su ma wasu daga cikin matasan da suka tuba da suka yi jawabi a wajen \u0199addamar da shirin, sun gode wa gwamnati bisa wannan tsari, tare da yin al\u0199awarin zama \u2019yan \u0199asa masu zaman lafiya da amfani a cikin al\u2019umma.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p style=\"text-align: left;\"><strong><em>Abdullahi Jalaluddeen<\/em><\/strong><\/p>\n<p style=\"text-align: left;\">\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano tare da ha\u0257in gwiwar Hukumar \u2019Yan Sanda ta \u0198asa sun kammala binciken\u00a0 matasa 718 da suka daina harkar daba a \u0199ar\u0199ashin shirin &#8216;Safe Corridor Project&#8217; na jihar. Wannan mataki muhimmin tsari ne na rage rashin tsaro da kuma bai wa matasa masu rauni damar zama nagari. Bikin \u0199addamar da shirin ya gudana [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":6021,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[576,39],"class_list":["post-6020","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-daba","tag-kano"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Police-Arrest-1583-Suspected-Thugs-Drug-Peddlers-In-Kano.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=6020"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":6022,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/6020\/revisions\/6022"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/6021"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=6020"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=6020"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=6020"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}