{"id":5994,"date":"2025-08-20T13:14:40","date_gmt":"2025-08-20T13:14:40","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5994"},"modified":"2025-08-20T13:16:40","modified_gmt":"2025-08-20T13:16:40","slug":"gwamna-yusuf-ya-rantsar-da-sabon-shugaban-hukumar-kar%c9%93ar-%c6%99orafe-%c6%99orafe-ta-jihar-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-yusuf-ya-rantsar-da-sabon-shugaban-hukumar-kar%c9%93ar-%c6%99orafe-%c6%99orafe-ta-jihar-kano\/","title":{"rendered":"Gwamna Yusuf Ya Rantsar Da Sabon Shugaban Hukumar Kar\u0253ar \u0198orafe-\u0199orafe Ta Jihar Kano"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barista Sa\u2019idu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kar\u0253ar \u0198orafe-\u0199orafe da Ya\u0199i da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC).<\/p>\n<p>An gudanar da wannan gajeren bikin ne a gidan gwamnati na Kano, inda Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari\u2019a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci rantsar da shi.<\/p>\n<p>Idan za a tuna Gwamna Yusuf ya gabatar da sunan Sa&#8217;idu Yahaya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da tabbatarwa bisa tsarin doka, inda daga bisani majalisar ta amince da nadin nasa.<\/p>\n<p>Barista Sa\u2019idu Yahaya \u0199wararren masani ne a fannin ya\u0199i da cin hanci, wanda ya goge a aikinsa shekaru sama da 18. Ya yi aiki a Hukumar Ya\u0199i da Cin Hanci da Sauran Laifuka Masu Ala\u0199a\u00a0 (ICPC), inda ya kware a bincike,\u00a0 da gano kadarori.<\/p>\n<p>Da yake taya shi murna, Gwamna Yusuf ya nuna kwarin gwiwa cewa Yahaya zai sake fasalta PCACC tare da \u0199arfafa jajircewar gwamnatin jihar wajen ya\u0199ar cin hanci da wanzar da gaskiya a cikin mulki.<\/p>\n<p>Ya yi kira a gare shi da ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya da adalci,\u00a0 inda ya \u0199ara jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tsayawa kan gaskiya da ri\u0199on amana a hidimar jama\u2019a.<\/p>\n<p>A jawabinsa bayan an rantsar da shi, Barista Yahaya ya yi al\u0199awarin tabbatar da amincewar da aka nuna gare shi, inda ya ce zai \u0199ara kaimi wajen rage cin hanci, dawo da kadarorin da aka wawure, da tabbatar da adalci ga dukkan jama\u2019ar Kano.<\/p>\n<p>Hukumar PCACC, wacce aka kafa domin kar\u0253ar \u0199orafe-\u0199orafen jama\u2019a da kuma ya\u0199ar cin hanci a matakin jiha, ana sa ran za ta taka muhimmiyar rawa a \u0199ar\u0199ashin shugabancin Sa&#8217;idu Yahaya wajen cike gibin da hukumomin tarayya suka bari.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Abdullahi Jalaluddeen\u00a0<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da Barista Sa\u2019idu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kar\u0253ar \u0198orafe-\u0199orafe da Ya\u0199i da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC). An gudanar da wannan gajeren bikin ne a gidan gwamnati na Kano, inda Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari\u2019a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, ya jagoranci rantsar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5995,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[39,1477],"class_list":["post-5994","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kano","tag-pcacc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0032.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5994","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5994"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5994\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5996,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5994\/revisions\/5996"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5995"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5994"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5994"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5994"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}