{"id":5974,"date":"2025-08-20T05:28:53","date_gmt":"2025-08-20T05:28:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5974"},"modified":"2025-08-20T05:28:53","modified_gmt":"2025-08-20T05:28:53","slug":"yan-bindiga-sun-kashe-mutane-27-a-jihar-katsina","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-27-a-jihar-katsina\/","title":{"rendered":"\u2018Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 27 A Jihar Katsina"},"content":{"rendered":"<p>\u2018Yan bindiga sun kutsa garin Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutane 27, suka jikkata wasu da dama tare da yin garkuwa da kimanin 15.<\/p>\n<p>Maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 sun isa kauyen da Asubahin fari a kan babura, inda suka fara kai hari a wani masallaci, sukayi harbin mai kan uwa da wabi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 16\u00a0 nan take.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5977\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0004-300x159.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"159\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0004-300x159.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0004.jpg 720w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Shaidu sun ce daga baya maharan sun shiga unguwannin kauyen, inda suka kashe karin mutane 11 tare da yin garkuwa da mata da dama ciki har da masu shayarwa.<\/p>\n<p>\u2018Yan bindigar sun kuma lalata gidaje, shaguna da motocin al\u2019umma yayin harin.<\/p>\n<p>Unguwar Mantau tana da tazarar kilomita 17 daga garin Malumfashi.<\/p>\n<p>Gwamnatin Katsina ta tabbatar da harin, amma ta ce adadin mutanen da aka kashe bai kai ba. Kwamishinan tsaron cikin gida, Muazu Danmusa, ya ce mutum 13 ne aka kashe, sai dai mazauna kauyen sun dage cewa sun binne gawarwaki 27.<\/p>\n<p>Wani mazaunin garin mai suna Inusa Ladan ya ce: \u201c<em>Mun yi jana\u2019izar wadanda aka kashe, gawarwaki 27 muka kirga.<\/em>\u201d<\/p>\n<p>Gwamnatin ta bayyana cewa harin ramuwar gayya ne, domin a baya mutanen kauyen sun yi kwanton bauna ga \u2018yan bindiga suka kashe da dama daga cikinsu.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5976\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0005-300x191.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"191\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0005-300x191.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0005-1024x653.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0005-768x490.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250820-WA0005.jpg 1080w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>A fusace, mazauna Karfi da wasu kauyuka sun toshe hanyar Malumfashi zuwa Funtua, inda suka yi tattaki mai nisan kilomita 10 zuwa Malumfashi don nuna rashin jin dadinsu.<\/p>\n<p>Daga bisani jami\u2019an tsaro sun tarwatsa masu zanga-zangar, tare da bada tabbacin cewa za a kamo maharan domin hukunta su.<\/p>\n<p>Karamar hukumar Malumfashi na fama da hare-haren \u2018yan bindiga a \u2018yan makonnin nan. \u2018Yan bindiga sun kai hari Gidan Maijimina, Gidan Barau da Gidan Hazo, inda suka kashe mutane, suka kuma yi garkuwa da wasu tare da sace dabbobi da kayayyaki.<\/p>\n<p>Yawaitar hare-haren ya tilasta al\u2019ummomi da dama a kudancin Katsina neman sulhu da \u2018yan bindiga domin su tsira.<\/p>\n<p>A watan Yuli, kauyuka da suka hada da Gidan Maijimina, Unguwar Gishiri, Koro da Gidan Dandaudu sun hada Naira miliyan 15 wanda suka bai wa \u2018yan bindiga domin\u00a0 samun damar yin noma.<\/p>\n<p>Mazauna kauyukan sun koka cewa gwamnati ta barsu cikin halin kaka-ni-ka-yi \u201c<em>Muna da zabin biyu ne kawai: ko mu yi sulhu da su ko mu gudu,\u201d<\/em> in ji Malam Ado Karfi wanda aka yi garkuwa da mahaifinsa sau biyu.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa ya sayar da gonaki biyu domin biyan kudin fansa har naira miliyan 3.5 cikin shekaru biyu.<\/p>\n<p><strong><em>Daga Isma&#8217;il Adamu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>\u2018Yan bindiga sun kutsa garin Unguwar Mantau a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina, inda suka kashe akalla mutane 27, suka jikkata wasu da dama tare da yin garkuwa da kimanin 15. Maharan dauke da bindigogi kirar AK-47 sun isa kauyen da Asubahin fari a kan babura, inda suka fara kai hari a wani masallaci, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5975,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[970,145],"class_list":["post-5974","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-hari","tag-katsina"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Katsina-map.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5974","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5974"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5974\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5978,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5974\/revisions\/5978"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5975"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5974"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5974"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5974"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}