{"id":5961,"date":"2025-08-18T14:20:44","date_gmt":"2025-08-18T14:20:44","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5961"},"modified":"2025-08-18T14:20:44","modified_gmt":"2025-08-18T14:20:44","slug":"an-cire-rai-daga-ceto-wadanda-suka-makale-a-karkashin-gine-gine-samakon-ambaliyar-ruwa-a-pakistan","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-cire-rai-daga-ceto-wadanda-suka-makale-a-karkashin-gine-gine-samakon-ambaliyar-ruwa-a-pakistan\/","title":{"rendered":"An Cire Rai Daga Ceto Wadanda Suka Makale A Karkashin Gine-gine Samakon Ambaliyar Ruwa A Pakistan"},"content":{"rendered":"<p>Masu aikin ceto a Pakistan sun sanar da cire rai daga yiwuwar iya ceto masu sauran lumfashi a \u0199ar\u0199ashin gine-ginen da suka rushe a zaftarewar lakar da \u0199asar ta gani sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliya, wanda kawo yanzu ya kashe mutanen da yawansu ya kai 344.<\/p>\n<p>Bayan tono mai zurfi a tarin laka da baraguzan gine-ginen da suka rushe, masu aikin ceton a yammcin jiya Lahadi sun ce babu tabbacin iya samun masu sauran numfashi a \u0199arkashin laka, a wani yanayi da har yanzu ake neman mutanen da yawansu ya haura 150 da suka yi \u0253atan dabo tun bayan ibtila\u2019in na \u0199arshen makon jiya.<\/p>\n<p>Tun daga Alhamis \u0257in makon jiya Pakistan ke ganin mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wani \u0253angare na \u0199a\u0199\u0199arfan ruwan da bisa al\u2019ada \u0199asashen kudancin Asia ke gani duk shekara, tun daga \u0199arshen watan Yuni zuwa farkon watan Satumba ko \u0199arshen Yuni, da akan ga zubar ruwa mai yawan gaske ha\u0257e da iska mai \u0199arfi da kuma tsawa, wanda a lokuta da dama ke haddasa asarar \u0257imbin rayuka.<\/p>\n<p>Tuni ambaliyar ta haddasa rushewar \u0257aruruwan gidaje yayin da \u0199auyuka da dama ruwa ya cikasu kuma suka rasa hanyar fita daga inda suke, kodayake lamarin ya fi tsananta a yankin Khyber na Lardin Pakhtunkhwan inda mutane 317 suka mutu.<\/p>\n<p>Bayanai sun ce gidaje da dama sun zama kango bayan da ambaliyar ta kashe dukkanin iyalan a gefe guda kuma masana ke garga\u0257in cewa a nan gaba ne za a ga zubar ruwan mafi yawa wanda galibi ke cika tekuna da kan kai ga tumbatsarsu.<\/p>\n<p>A yankin Buner mutane 150 suka \u0253ace yayin da wasu 208 suka mutu, sannan aka shafe kauyuka 10 zuwa 12.<\/p>\n<p>Kamfanin dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa jami\u2019an agaji a\u0199alla dubu biyu ke aikin ceto.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>rfi<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Masu aikin ceto a Pakistan sun sanar da cire rai daga yiwuwar iya ceto masu sauran lumfashi a \u0199ar\u0199ashin gine-ginen da suka rushe a zaftarewar lakar da \u0199asar ta gani sakamakon mamakon ruwan sama da ya haddasa ambaliya, wanda kawo yanzu ya kashe mutanen da yawansu ya kai 344. Bayan tono mai zurfi a tarin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5962,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[320,830],"class_list":["post-5961","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ambaliya","tag-pakistan"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/250817-pakistan-flood-vl-940a-1ca8fa.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5961","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5961"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5961\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5963,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5961\/revisions\/5963"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5962"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5961"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5961"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5961"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}