{"id":5909,"date":"2025-08-16T18:03:23","date_gmt":"2025-08-16T18:03:23","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5909"},"modified":"2025-08-16T18:03:23","modified_gmt":"2025-08-16T18:03:23","slug":"za-a-sabunta-filin-jiragen-sama-na-ilori-zuwa-cibiyar-jigilar-kayayyaki-ta-zamani","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/za-a-sabunta-filin-jiragen-sama-na-ilori-zuwa-cibiyar-jigilar-kayayyaki-ta-zamani\/","title":{"rendered":"Za A Sabunta Filin Jiragen Sama Na Ilori Zuwa Cibiyar Jigilar Kayayyaki Ta Zamani"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi ha\u0257in gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta \u0198asa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci.<\/p>\n<p>Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da Hukumar FAAN ta shirya domin sanar da shirin fara jigilar kayayyaki a Filin Jiragen Sama na \u0198asa da \u0198asa na Janar Tunde Idiagbon da ke Ilori.<\/p>\n<p>A cewarsa, wannan shiri na nufin kara inganta matsayin jihar tare da \u0199arfafa rawar da take takawa a harkokin kasuwanci na cikin gida da waje.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa aikin ya yi daidai da manufofin wannan gwamnati na bu\u0257e sababbin hanyoyin fitar da kayayyaki, bun\u0199asa harkokin kasuwanci, da kuma \u0199ara samun ku\u0257a\u0257en shiga ga masu samar da kayayyaki da\u00a0 \u2018yan kasuwa.<\/p>\n<p>Dakta Abolore ya ce jigilar kayayyakin ta jiragen zai sau\u0199a\u0199a daukarsu daga gonaki, zuwa masana\u2019antu, da wuraren sana\u2019o\u2019i zuwa kasuwannin cikin gida da na \u0199asashen waje, wanda hakan zai\u00a0 \u0199ara musu daraja, sarrafawa da a fannoni daban-daban.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya bayyana cewa shirin zai rage asara, ya kiyaye ingancin kayayyaki, sannan ya bun\u0199asa damar kasuwanci a fannin kayayyakin gona, masana\u2019antu, da kayayyakin da aka sarrafa.<\/p>\n<p>Ya nuna cewa saboda cunkoson da ake samu a tashoshin jiragen sama da na ruwa da ke\u00a0 Legas, garin Ilori na wata dama ta musamman wajen samun fitar da kayayyaki cikin lokaci da inganci, tare da \u0199ara wa jihar damar gogayya da jihohi da ma kasashen duniya.<\/p>\n<p>Dakta Abolore ya yi kira ga manoma, \u0199ungiyoyi, masu masana\u2019antu, masu saka jari, \u0199ungiyoyin sufuri, \u2018yan kasuwa, masu sarrafawa, da hukumomin da ke kula da doka da tsari, da su ha\u0257a kai wajen kara inganci, yadda ake shirya kayayyaki daidai da zamani, da amfani da fasaha domin bin ka\u2019idojin kasuwannin \u0199asashen waje.<\/p>\n<p>Shi ma Manajan Filin Jirgin Sama na Janar Tunde Idiagbon, Mista Suraju Aderibigbe, ya bayyana cewa za a sabunta tsohon ginin tashar zuwa sabuwar cibiyar jigilar kaya mai amfani da fasahohi na zamani domin tabbatar da tsaro wajen sarrafa nau\u2019ukan kayayyaki daban-daban.<\/p>\n<p>Ya tabbatar da cewa wannan gyara zai \u0199ara bun\u0199asa kasuwanci, samar da ayyukan yi, da kuma ci gaban tattalin arziki a fannoni da dama a jihar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Ali Muhammad Rabi&#8217;u\u00a0<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kwara ta ce za ta yi ha\u0257in gwiwa da Hukumar Filayen Jiragen Sama ta \u0198asa (FAAN) da sauran masu ruwa da tsaki domin mayar da jihar cibiyar fitar da kayan gona da na kasuwanci. Kwamishinan Noma da Ci gaban Karkara na jihar, Dakta Afees Abolore, ne ya bayyana haka a wani taron da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5911,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,10,9],"tags":[1460,175],"class_list":["post-5909","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","category-tattalin-arziki","tag-filin-jiragen-sama","tag-kwara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/sddefault.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5909","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5909"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5909\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5912,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5909\/revisions\/5912"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5911"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5909"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5909"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5909"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}