{"id":5888,"date":"2025-08-14T22:08:06","date_gmt":"2025-08-14T22:08:06","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5888"},"modified":"2025-08-14T22:08:06","modified_gmt":"2025-08-14T22:08:06","slug":"gwamnatin-tarayya-ta-amince-da-gina-asibitin-dabbobi-a-jihar-kwara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-tarayya-ta-amince-da-gina-asibitin-dabbobi-a-jihar-kwara\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara"},"content":{"rendered":"<p>Ministan Ma&#8217;aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara.<\/p>\n<p>Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar\u00a0 a Ilori babban birnin Jihar Kwara.<\/p>\n<p>Da yake wakiltar Ministan, Richard Mbaram ya bayyana wannan shiri a matsayin babbar nasara a tarihi wajen samo mafita ta dindindin ga rikicin manoma da makiyaya a \u0199asar nan.<\/p>\n<p>Ya ce aikin na daga cikin tsare-tsaren Shirin Sauya Hanyar Kiwo na Kasa (National Livestock Transformation Plan) na tsawon shekaru goma (2019-2028) wanda ya mayar da hankali kan gyara harkar kiwo a Najeriya.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Kwamishinan \u0198asa na L-Press, Dr. Sanusi Abubakar, ya yaba wa Jihar Kwara bisa zuba jari a bangaren ci gaban kiwo.<\/p>\n<p>Ya yi alkawarin ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya domin cimma sabon tsari a harkar kiwo.<\/p>\n<p>Shi ma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, wanda Mai ba shi Shawara na Musamman Alhaji Sa&#8217;adu Salahudeen, ya wakilta, ya yaba wa cibiyar cike ta Jami\u2019ar Bayero Kano bisa jajircewa da \u0199warewar da suka nuna a duk tsawon aikin.<\/p>\n<p>Ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta aiwatar da sakamakon binciken ba tare da kaucewa daga abin da aka gano ba.<\/p>\n<p>Gwamna AbdulRazaq ya yi kira ga sarakuna, abokan hulda, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su hada hannu da gwamnati wajen aiwatar da shawarwarin da binciken ya bayar.<\/p>\n<p>Tun da farko a jawabinsa, Darakta a\u00a0 Cibiyar Harkar Noma ta Jami\u2019ar Bayero da ke Kano, Farfesa Sanusi Muhammed, ya bayyana cewa binciken ya samar da wani dandali mai inganci don tsara ayyuka, kai agaji, da \u0199ir\u0199irar manufofi a bangaren kiwo.<\/p>\n<p>Farfesa Muhammed ya yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da bayanan taswirar wajen\u00a0 gyaran ruwan sha na dabbobi da \u0199ir\u0199irar tsarin samar da ruwa mai jure canjin yanayi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>ALI MUHAMMAD RABIU<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Ministan Ma&#8217;aikatar Kula da Kiwon Dabbobi, Alhaji Idi Mukhtar Maiha, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da gina sabon asibitin dabbobi, da cibiyar ajiye dabbobi, tare da samar da allurar rigakafi a Jihar Kwara. Ministan ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon nazarin taswirar fadin jihar(Geospatial Mapping) da aka gudanar\u00a0 a Ilori babban [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5889,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,10],"tags":[1261,175],"class_list":["post-5888","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","tag-dabbobi","tag-kwara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250814-WA0049.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5888","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5888"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5888\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5890,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5888\/revisions\/5890"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5889"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5888"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5888"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5888"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}