{"id":5774,"date":"2025-08-11T21:37:01","date_gmt":"2025-08-11T21:37:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5774"},"modified":"2025-08-11T21:38:34","modified_gmt":"2025-08-11T21:38:34","slug":"tinubu-ya-jinjinawa-nafdac-bisa-matsayin-da-ta-taka-a-hukumar-lafiya-ta-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tinubu-ya-jinjinawa-nafdac-bisa-matsayin-da-ta-taka-a-hukumar-lafiya-ta-duniya\/","title":{"rendered":"Tinubu Ya Jinjinawa NAFDAC Bisa Matsayin Da Ta Taka A Hukumar Lafiya Ta Duniya"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta \u0198asa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da ri\u0199e matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi.<\/p>\n<p>Mai Ba Shugaban \u0198asa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka\u2019idojin \u0199asa da \u0199asa.<\/p>\n<p>Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da \u0199asashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara.<\/p>\n<p>Wannan sabon tantancewa ya biyo bayan wani binciken ne\u00a0 a watan Nuwamban 2024, tare da gudanar da tarukan duba Shirin Cigaban Cibiyoyi(IDP) guda biyar tsakanin Fabrairu zuwa Afriln 2025 domin tantance matakan gyara. WHO ta yaba wa NAFDAC kan ci gaba da samun tsari mai \u0199arfi, da ke aiki yadda ya kamata, tare da yaba wa goyon bayan gwamnati wajen \u0199arfafa hukumar.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya jinjina wa shugabanni da ma\u2019aikatan NAFDAC bisa \u0199warewa da sadaukarwa, yana mai cewa wannan nasara ta \u0199ara \u0257aukaka matsayin Najeriya a fannin kula da\u00a0 lafiya da shirin kare cututtuka.<\/p>\n<p>Ya ce wannan nasara na daidai da kudirin gwamnatinsa na Renewed Hope Agenda domin sauya tsarin kula da lafiya.<\/p>\n<p>Shugaban ya yi nuni da ci gaba da ake samu, ciki har da inganta\u00a0 cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 17,000, kyautata kulawa da mata masu juna biyu da na\u2019urorin gano cututtuka a yankunan da ba su da iisassun kayayyakin kula da lafiya, horar da ma\u2019aikatan lafiya 120,000, da kuma ninka yawan masu amfani da shirin\u00a0 inshorar lafiya na \u0199asa cikin shekaru uku.<\/p>\n<p>Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta \u0199arfafa samar da kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida da jawo ra&#8217;ayin masu zuba jari a fannin lafiya.<\/p>\n<p>Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa NAFDAC a yunkurinta na cimma matsayin WHO Maturity Level 4, mafi girma a duniya kan ingancin sarin kula da magunguna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban \u0198asa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta \u0198asa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da ri\u0199e matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi. Mai Ba Shugaban \u0198asa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5776,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[923,89],"class_list":["post-5774","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-nafdac","tag-tinubu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/nafdac.png","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5774","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5774"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5774\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5775,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5774\/revisions\/5775"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5776"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5774"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5774"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5774"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}