{"id":5761,"date":"2025-08-11T14:01:59","date_gmt":"2025-08-11T14:01:59","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5761"},"modified":"2025-08-11T14:01:59","modified_gmt":"2025-08-11T14:01:59","slug":"unicef-da-gavi-sun-bada-naurorin-samar-da-wutar-lantarki-ta-hasken-rana-ga-jihar-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/unicef-da-gavi-sun-bada-naurorin-samar-da-wutar-lantarki-ta-hasken-rana-ga-jihar-kano\/","title":{"rendered":"UNICEF Da Gavi Sun Bada Na\u2019urorin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana Ga Jihar Kano"},"content":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da ha\u0257in gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na\u2019urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin \u0199arfafa rigakafin yara da kuma kula da lafiyar jama\u2019a.<\/p>\n<p>A yayin bikin mika kayayyakin ga gwamnatin jihar da Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta \u0198asa (NPHCDA), Kwamishinan Lafiya na Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya ce wannan shiri na nufin taimaka wa yaran da ba a musu rigakafi, da mata masu juna biyu da ba su da damar samun rigakafin yau da kullum da kuma wasu ayyukan kiwon lafiya.<\/p>\n<p>\u201cUNICEF tare da Gavi, \u0199ar\u0199ashin shirin \u0199arfafa tsarin kiwon lafiya na CDS3, sun tallafa wajen saka na\u2019urorin hasken rana a cibiyoyin PHC na kananan hukumomin da ke da yawan yaran da ba a musu rigakafi a Najeriya.\u201d In ji Dakta Labaran.<\/p>\n<p>Ya ce Kano ce ta fi kowace jiha a Najeriya yawan yaran da ba a taba yi wa rigakafi ba, yana mai jaddada cewa cibiyoyin da aka saka musu wadannan na&#8217;urorin za su taka muhimmiyar rawa wajen kawar da matsalar.<\/p>\n<p>Wannan aiki ya biyo bayan binciken yadda cibiyoyin lafiya a matakin farko ke aiki da wutar lantarki da UNICEF ta tallafa a shekarar 2023, wanda ya gano cibiyoyi 371 da suka cancanci a saka musu na\u2019urorin. A wannan matakin, tare da ha\u0257in gwiwar eHealth Systems Africa, an samar da wutar hasken rana a cibiyoyi 28 a Kano.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5762\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250811-WA0015-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250811-WA0015-300x225.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250811-WA0015-768x576.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250811-WA0015.jpg 1016w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Tsarin za\u0253en cibiyoyin ya mayar da hankali kan cibiyoyin kiwon lafiya a kananan hukumomin da ke da yawan yaran da ba a musu\u00a0 rigakafi, tare da cire wa\u0257anda wasu ayyuka irin su CRIBS da IMPACT suka riga suka rufe, da kuma mayar da hankali kan cibiyoyin da ba su da ingantacciyar wutar lantarki.<\/p>\n<p>Dakta Labaran ya gargadi jami\u2019an da ke kula da cibiyoyin da kada su karkatar da su don amfani na kashin kansu.<\/p>\n<p>Daraktan \u0198asa na Gavi, Jessica Crawford, ta bayyana cewa wannan karamcin wani \u0253angare ne na \u0199o\u0199arin ha\u0257in gwiwa don \u0199arfafa tsarin kiwon lafiya a Kano, inda ta \u0199ara da cewa Gavi za ta kashe kusan dala miliyan biyar a jihar cikin shekara biyu masu zuwa domin tallafawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati wajen inganta lafiyar mata da yara.<\/p>\n<p>Mai ri\u0199on mukamin Shugaban Ofishin UNICEF a Kano, Michael Banda, wanda ya wakilci Shugaban Ofishin, Mista Rahama Rihood Mohammed Farah, ya bayyana shirin a matsayin mataki na gina tsarin kiwon lafiya mai \u0257orewa da adalci ga kowa.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa samun wutar lantarki mai inganci na taimakawa wajen adana rigakafi yadda ya kamata, yin aiki a kowane lokaci, da rage dogaro da man fetur.<\/p>\n<p>Taron ya samu halartar Darakta Janar na Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano, Farfesa Salisu Ibrahim, da wakilai daga WHO, Gidauniyar Gates, da sauran abokan ha\u0257in gwiwa.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) tare da ha\u0257in gwiwar Gavi da ke taimakawa wajen samar da rigakafi, sun mika na\u2019urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana g Gwamnatin Jihar Kano domin amfani da su a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) guda 28 da nufin \u0199arfafa rigakafin yara da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5763,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[1438,39,704],"class_list":["post-5761","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-gavi","tag-kano","tag-unicef"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250811-WA0014.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5761","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5761"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5761\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5764,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5761\/revisions\/5764"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5763"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5761"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5761"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5761"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}