{"id":5684,"date":"2025-08-07T23:04:32","date_gmt":"2025-08-07T23:04:32","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5684"},"modified":"2025-08-07T23:04:32","modified_gmt":"2025-08-07T23:04:32","slug":"unicef-ya-samar-da-abinci-mai-gina-jiki-ga-yara-sama-da-17000-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/unicef-ya-samar-da-abinci-mai-gina-jiki-ga-yara-sama-da-17000-a-kano\/","title":{"rendered":"UNICEF Ya Samar Da Abinci Mai Gina Jiki Ga Yara Sama Da 17,000 A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke \u0199asa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke \u0199ara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari.<\/p>\n<p>Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar ha\u0257in gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin <strong>Child Nutrition Match Fund<\/strong>, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai.<\/p>\n<p>Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma saboda rashin abinci mai gina jiki, yayin da sama da kashi 10 suke fama da matsalar rashin nauyi da zai ba su kuzari.<\/p>\n<p>A cewarsa, <strong>Child Nutrition Match Fund<\/strong> shiri ne da UNICEF ke kula da shi, tare da goyon bayan masu bayar da tallafin \u0199asashen waje, inda ake bayar da ku\u0257i daidai-da-daidai (1:1 match funding) domin ninka jarin da gwamnatoci ke sakawa wajen samar da muhimman kayan abinci mai gina jiki.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5687\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250808-WA0001-300x169.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"169\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250808-WA0001-300x169.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250808-WA0001-768x432.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250808-WA0001.jpg 1020w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Ya bayyana cewa Jihar Kano ta zama jagora a \u0199asa wajen wannan \u0199o\u0199ari, inda ta bayar da gudummawar Naira miliyan 500 \u2013 mafi girma daga jiha guda \u2013 zuwa wannan asusu. Haka kuma shi ma asusun na UNICEF ya \u0199ara Naira miliyan 500, wanda ya kawo jimillar Naira biliyan 1. Wannan ku\u0257in aka yi amfani da shi wajen sayen kwalaye 12,948 na hadin abinci mai gina jiki da zai warkar da\u00a0 yara sama da 17,000 masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.<\/p>\n<p>Dakta Deres ya bayyana cewa UNICEF na fassara <strong>child food poverty<\/strong> a matsayin rashin damar samun abinci mai gina jiki, mai yalwa, da kuma bambancin sinadaran gina jiki ga yara &#8216;yan \u0199asa da shekaru biyar \u2013 wani lokaci mai matu\u0199ar muhimmanci wajen ha\u0253akar jiki da kwakwalwa.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa UNICEF tare da hadin gwiwar masu tallafi sun samu gagarumar nasara wajen inganta abinci mai gina jiki a fa\u0257in Najeriya, musamman a Kano.<\/p>\n<p>Ya yabawa jagorancin gwamnati tare da kira ga Gwamnan Jihar Kano da ya ware \u0199arin ku\u0257i a shekarar 2025, wanda UNICEF za ta sake bada kwatankwacinsa domin a sake sayen sinadirai da kayayyakin abincin.<\/p>\n<p>Haka kuma ya bukaci a amince da manufofin bayar da hutun haihuwa na tsawon watanni shida mai ga matan da suka haihu, domin \u0199arfafa shayar da jarirai nono zalla da kuma kare lafiyar jarirai da abincinsu.<\/p>\n<p>Asusun na UNICEF ya sake jaddada aniyar sa ta tallafawa Jihar Kano ta hanyar ha\u0257in gwiwar dabaru masu fa\u0257i a fannoni daban-daban domin inganta abinci mai gina jiki da lafiyar al\u2019umma musamman ga mata da yara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><b><em>Daga Khadijah Aliyu<\/em>\u00a0<\/b><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke \u0199asa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke \u0199ara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5686,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[39,704],"class_list":["post-5684","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kano","tag-unicef"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250808-WA0002.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5684","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5684"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5684\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5688,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5684\/revisions\/5688"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5686"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5684"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5684"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5684"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}