{"id":5646,"date":"2025-08-07T09:44:51","date_gmt":"2025-08-07T09:44:51","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5646"},"modified":"2025-08-07T11:11:27","modified_gmt":"2025-08-07T11:11:27","slug":"matasan-kauru-sun-zargin-dan-majalisar-dokoki-barnabas-danmaigona-da-rashin-tabuka-komai","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/matasan-kauru-sun-zargin-dan-majalisar-dokoki-barnabas-danmaigona-da-rashin-tabuka-komai\/","title":{"rendered":"Matasan Kauru Sun Zargi Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin Tabuka Komai"},"content":{"rendered":"<p>Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken &#8216;<strong><em>Daga Fata zuwa Yaudara&#8217;<\/em><\/strong> wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma \u0257an siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al\u2019umma.<\/p>\n<p>Sanarwar ta koka da yadda al\u2019ummar Kauru suka sanya kyakkyawan fata a shugabancin Danmaigona, amma a maimakon haka, ya kasa ba marada kunya.<\/p>\n<p>Har ila yau, ta yi Allah-wadai da kawancen siyasarsa da Mukhtar Chawai, wani dan siyasa da aka ce ko ake zargin bai tabuka komai a mazabarsa ba, tare da bayyana cewa irin wannan kawancen yana kashe musu gwiwa matukar gaske.<\/p>\n<p>KYA ta bayyana rashin jin dadin ta a kan abin da suka kira wasu &#8216;yan kudaden da basu gaza dubu 5 zuwa 10 da yake rabawa jama&#8217;a a matsayin yankawa kare ciyawa domin wannan ba abin da suke tsinanawa al&#8217;ummar da yake wakilta<\/p>\n<p>Saboda haka Kungiyar ta bukaci al\u2019ummar mazabar Kauru da su tashi tsaye akan nuna halin ko-in-kula a siyasance, su nemi wakilcin da ya dace, sannan su ki yarda a ba su kyauta irin wannan da bata tsinana musu komai.<\/p>\n<p>Sun yi nuni da \u2018yan majalisa irin su Hon. Shehu Yunusa na Kubau, wanda rahotanni suka ce ya ba da fifiko wajen hada kai da ci gaba, a matsayin misalan yadda wakilci na gaskiya ya kasance.<\/p>\n<p>Da take kira da a wayar da kan \u2018yan siyasa da kuma daukar matakin gama gari, sanarwar ta kalubalanci matasa da masu kada kuri\u2019a a Kauru da su yi wa shugabanninsu hisabi, inda ta dage cewa zabe aiki ne..<\/p>\n<p>KYA ta bayyana cewa Hon. Danmaigona ya samu damarsa, kuma har yanzu jama\u2019a na nan suna jira, ba wai kawai alkawura ba, a\u2019a, a samu canji na zahiri.<\/p>\n<p><strong><em>Rel\/Yusuf Zubairu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken &#8216;Daga Fata zuwa Yaudara&#8217; wanda [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":18,"featured_media":5654,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,2],"tags":[1426,1424,1427,211,341,1425],"class_list":["post-5646","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-siyasa","tag-danmaigona","tag-kauru","tag-kya","tag-majalisa","tag-matasa","tag-zargi"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/Kauru_1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5646","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/18"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5646"}],"version-history":[{"count":6,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5646\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5655,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5646\/revisions\/5655"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5654"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5646"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5646"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5646"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}