{"id":5635,"date":"2025-08-06T13:37:56","date_gmt":"2025-08-06T13:37:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5635"},"modified":"2025-08-06T13:37:56","modified_gmt":"2025-08-06T13:37:56","slug":"tinubu-ya-umurci-a-bada-kulawar-lafiya-kyauta-ga-tsofaffin-maaikata-masu-karamin-fansho","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/tinubu-ya-umurci-a-bada-kulawar-lafiya-kyauta-ga-tsofaffin-maaikata-masu-karamin-fansho\/","title":{"rendered":"Tinubu Ya Umurci A Bada Kulawar Lafiya Kyauta Ga Tsofaffin Ma\u2019aikata Masu Karamin Fansho"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban \u0199asa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma\u2019aikata masu \u0199aramin albashi da ke \u0199ar\u0199ashin tsarin fansho na ha\u0257in gwiwa (Contributory Pension Scheme \u2013 CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare\u00a0 da zai taimaka wa rayuwarsu.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai ba Shugaban \u0199asa shawara na musamman kan harkokin ya\u0257a labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi \u0199arancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma\u2019aikata mafi rauni a tsarin CPS.<\/p>\n<p>Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho ta \u0198asa (PenCom), Ms. Omolola Oloworaran, ta gabatar wa Shugaban \u0199asa.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya kuma umurci Daraktar Janar ta PenCom din da ta gaggauta warware matsalar fanshon \u2019yan sanda da ta da\u0257e tana ci gaba, yana mai jaddada cewa \u2019yan sanda samar da tsaro a \u0199asa suna da hakkin samun fansho cikin mutuntawa da kwanciyar hankali.<\/p>\n<p>Daraktar Janar din ta kuma sanar da Shugaban \u0199asa yadda ake \u0199o\u0199arin kare darajar asusun fansho duba da hauhawar farashi da matsin tattalin arziki, da kuma shirin kaddamar da tsarin ba da gudummawar fansho da kudin waje domin bai wa \u2019yan Najeriya mazauna \u0199asashen waje damar shiga tsarin fansho.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya nuna cikakken goyon bayansa ga wa\u0257annan gyare-gyare, yana mai sake jaddada aniyar gwamnatinsa na bun\u0199asa ci gaba mai \u0257orewa da kare rayuwar talakawan Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Bello Wakili<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban \u0199asa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma\u2019aikata masu \u0199aramin albashi da ke \u0199ar\u0199ashin tsarin fansho na ha\u0257in gwiwa (Contributory Pension Scheme \u2013 CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare\u00a0 da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":3657,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[89,1423],"class_list":["post-5635","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-tinubu","tag-tsofaffin-maaikata"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/03\/President-Bola-Tinubu-portrait-750x430-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5635","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5635"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5635\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5636,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5635\/revisions\/5636"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3657"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5635"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5635"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5635"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}