{"id":5632,"date":"2025-08-06T13:13:31","date_gmt":"2025-08-06T13:13:31","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5632"},"modified":"2025-08-06T13:13:31","modified_gmt":"2025-08-06T13:13:31","slug":"malaman-jamioin-israila-sun-nemi-jamus-ta-tilasta-dakatar-da-yakin-gaza","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/malaman-jamioin-israila-sun-nemi-jamus-ta-tilasta-dakatar-da-yakin-gaza\/","title":{"rendered":"Malaman Jami&#8217;o&#8217;in Isra&#8217;ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza"},"content":{"rendered":"<p>Malaman jami&#8217;o&#8217;i sama da 100 daga Isra&#8217;ila sun bayyana cewar jan kafar da \u0199asar Jamus ke yi wajen \u0257aukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra&#8217;ila na iya bai wa \u0199asar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza.<\/p>\n<p>Wata wasika da masanan suka rubuta wa \u0257aya daga cikin manyan shugabannin jam&#8217;iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin \u0257aukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya.<\/p>\n<p>A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam&#8217;iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci \u0199asar da ta shiga cikin \u0199asashen duniya da ke \u0199awance domin gaggauta kawo \u0199arshen ya\u0199in Gaza da kuma sanya takunkumi a kan Isra&#8217;ila da kuma kin sayar mata da makamai.<\/p>\n<p>Gwamnatin Jamus da ke \u0199ar\u0199ashin \u0199awance jam&#8217;iyyun CDU da SCU da kuma SPD ta \u0199arfafa sukar da take yiwa gwamnatin Isra&#8217;ila a kan yadda take azabtar da mazauna Gaza wajen hana kai musu kayan agaji, amma kuma ya zuwa yanzu bata bayyana \u0257aukar wasu matakai masu tsauri ba.<\/p>\n<p>Isra&#8217;ilar dai ta yi watsi da duk wani yunkuri na zargin da ake mata na amfani da yunwa wajen azabtar da mutane akalla miliyan biyu dake zama a Gaza, inda ta bayyana cewar \u0199ungiyar Hamas ce ke sace abincin da ake kai wa mutanen yankin.<\/p>\n<p>Matakan kai hari a kan masu neman kayan agajin da Isra&#8217;ila ke yi a kan mazauna Gazar, sun yi sanadiyar hallaka akalla mutane sama da dubu guda.<\/p>\n<p>Kungiyar Hamas ta \u0199addamar da harin da ya hallaka Yahudawa sama da 1,200 a watan Oktobar shekarar 2023, abinda ya sa Isra&#8217;ila \u0199addamar da yakin da ya hallaka mutane sama da 50,000 a bangaren Falasdinawa.<\/p>\n<p>Tuni \u0199asashen Birtaniya da Canada da kuma Faransa suka bayyana aniyarsu ta amincewa da \u0199asar Falasdinu a taron Majalisar \u018ainkin Duniyar da zai gudana a watan Satumba, inda suke cewa ta wannan hanyar ce kawai za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.<\/p>\n<p>Isra&#8217;ila da Amurka sun bayyana matu\u0199ar \u0253acin ransu da matakin, yayin da a yau Firaminista Benjamin Netanyahu ke cewa ba zai dakatar da yakin da yake yi ba har sai ya murkushe \u0199ungiyar Hamas.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Malaman jami&#8217;o&#8217;i sama da 100 daga Isra&#8217;ila sun bayyana cewar jan kafar da \u0199asar Jamus ke yi wajen \u0257aukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra&#8217;ila na iya bai wa \u0199asar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa \u0257aya daga cikin manyan shugabannin jam&#8217;iyyar SPD da ke [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5633,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[70,1422],"class_list":["post-5632","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-gaza","tag-malam-jamia"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/fcf4516_sirius-fs-upload-1-cyzwiluzaket-1746088079179-301862.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5632","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5632"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5632\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5634,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5632\/revisions\/5634"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5633"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5632"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5632"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5632"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}