{"id":5613,"date":"2025-08-06T10:45:46","date_gmt":"2025-08-06T10:45:46","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5613"},"modified":"2025-08-06T10:45:46","modified_gmt":"2025-08-06T10:45:46","slug":"batun-ceto-wanda-ake-zargi-da-kwaya-kwamishinan-kano-ya-yi-murabus","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/batun-ceto-wanda-ake-zargi-da-kwaya-kwamishinan-kano-ya-yi-murabus\/","title":{"rendered":"Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus"},"content":{"rendered":"<p>Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kar\u0253i rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.<\/p>\n<p>Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma \u0257aukar nauyin ayyukanta a bainar jama&#8217;a.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al\u2019amuran da suka shafi jama\u2019a da kuma halin da ake ciki.<\/p>\n<p>Ya ce: <em>\u201cA matsayina na \u0257aya daga cikin masu fada-a-ji a wannan gwamnati da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, ya dace na \u0257auki wannan mataki, koda kuwa zai sosa zukata.<br \/>\n\u201cKo da yake ina ci gaba da musanta hannuna a lamarin, ba zan iya watsi da irin yadda jama\u2019a ke kallon batun ba, da kuma bukatar kare \u0199imar gwamnati da muka ginata tare.\u201d<\/em> In ji shi.<\/p>\n<p>Alhaji Namadi ya nuna godiya ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda ba shi damar yi wa jiharsa hidima, tare da jaddada aniyarsa ta ci gaba da bin manufofin gwamnatin.<\/p>\n<p>Ya \u0199ara da cewa: <em>\u201cA matsayina na \u0257an \u0199asa nagari, dole ne in ci gaba da kare amana da hangen nesan da muka ha\u0257a kai wajen shimfi\u0257awa a\u00a0 jiharmu. Zan ci gaba da kasancewa mai biyayya ga akidun da suka kawo wannan gwamnati kan mulki.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kar\u0253i murabus \u0257in cikin farin ciki, tare da yi masa fatan alheri a duk wani yun\u0199urinsa na gaba.<\/p>\n<p>Gwamnan ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa wajen tabbatar da adalci, ladabi, da kuma yaki da miyagun dabi\u2019u da laifukan da suka shafi kwayoyi da sauran matsalolin da ke shafan matasa da al\u2019umma baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Ya kuma ja hankalin duk masu rike da mukaman siyasa da su kasance masu hikima da taka-tsantsan wajen hul\u0257a da al\u2019amuran jama\u2019a, tare da neman izini daga hukumomi mafi girma kafin su shiga cikin wani lamari da ke da tasiri a bainar jama\u2019a.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Abdullahi Jalaluddeen<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kar\u0253i rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5614,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[39,703,1420],"class_list":["post-5613","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kano","tag-kwamishina","tag-murabus"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250806-WA0005.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5613","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5613"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5613\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5615,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5613\/revisions\/5615"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5614"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5613"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5613"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5613"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}