{"id":5573,"date":"2025-08-04T13:43:01","date_gmt":"2025-08-04T13:43:01","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5573"},"modified":"2025-08-04T13:43:01","modified_gmt":"2025-08-04T13:43:01","slug":"gwamna-abdulrazaq-ya-amince-da-naira-biliyan-20-don-gyaran-gine-ginen-makarantu-a-kwara","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-abdulrazaq-ya-amince-da-naira-biliyan-20-don-gyaran-gine-ginen-makarantu-a-kwara\/","title":{"rendered":"Gwamna AbdulRazaq Ya Amince Da Naira Biliyan 20 Don Gyaran Gine-ginen Makarantu A Kwara"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati.<\/p>\n<p>Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka\u00a0 zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin.<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko.<\/p>\n<p>Ta kara da cewa gwamnatin ta gyara sama da ajujuwa 1,254 banda wasu muhimman ayyukan gyara da aka gudanar a wurare daban-daban.<\/p>\n<p>Gwamnatin ta bayyana jin dadinta kan aiwatar da ayyukan gyaran makarantu na SUBEB-UBEC tun daga shekarar 2014.<\/p>\n<p>Sanarwar ta ce wannan sabuwar gudummawar za ta hada da dakunan gwaje-gwaje da wuraren tsafta a makarantun da ke sassa daban-daban na jihar, domin cike gibi tare da kara karfafa ayyukan da SUBEB ke yi.<\/p>\n<p>&#8220;<em>Duk da irin manyan ayyukan da muka gudanar, muna sane da cewa har yanzu akwai gibin da ake bukatar cikewa, kuma wannan ne dalilin da ya sa Mai Girma Gwamna ya amince da wannan sabon matakin na musamman don rage gibin da ke cikin gine-ginen makarantu<\/em>,&#8221; In ji sanarwar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Ali Muhammad Rabi\u2019u<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5574,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11],"tags":[175,155],"class_list":["post-5573","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kwara","tag-makarantu"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250804-WA0019.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5573","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5573"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5573\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5575,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5573\/revisions\/5575"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5574"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5573"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5573"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5573"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}