{"id":5531,"date":"2025-08-03T22:25:56","date_gmt":"2025-08-03T22:25:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5531"},"modified":"2025-08-03T22:25:56","modified_gmt":"2025-08-03T22:25:56","slug":"gwamnatin-jigawa-ta-dauki-manyan-matakan-kare-jihar-daga-ambaliyar-ruwa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-jigawa-ta-dauki-manyan-matakan-kare-jihar-daga-ambaliyar-ruwa\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Jigawa Ta Dauki Manyan Matakan Kare Jihar Daga Ambaliyar Ruwa"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al&#8217;umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana.<\/p>\n<p>Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu.<\/p>\n<p>Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al\u2019umma.<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana cewar, Gwamna Namadi ya inganta harkar noma don tabbatar da isasshen abinci da samar da ayyukan yi ga al\u2019ummar karkara.<\/p>\n<p>A cewar sa, kwamitin fasaha na magance ambaliya ya zage damtse wajen sarrafa koguna da gina kwarya-kwaryar shinge a wuraren da ake sa ran ambaliya domin magance matsalar.<\/p>\n<p>A don haka, Hamza Muhammad Hadejia, ya bukaci jama\u2019a su ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga gwamnatin jihar domin a cimma wannan manufa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.<\/p>\n<p>ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da ya ke baiwa ayyukan kwamitin a kowane lokaci.<\/p>\n<p>A jawaban su, Dagacin Turabu Malam Shu\u2019aibu Saje da Shugaban ci gaban al\u2019umma Sani Barde da tsohon kansila Umar Jiyan, sun jinjinawa Gwamna Umar Namadi da shugaban karamar hukumar Auyo da mai ba da shawara Hamza Hadejia bisa kokarin kare rayuka da dukiyoyin su, tare da tabbatar da gudunmawar su don cimma burin gwamnati kan magance ambaliya a yankin.<\/p>\n<p>Sun kuma godewa gwamnatin jihar Jigawan da ta kananan hukumomi bisa samar da ababen more rayuwa da kuma bunkasa harkokin ilimi da lafiya da ruwa da wuta da hanyoyi da kuma bunkasa noma don samar da isasshen abinci da ayyykan yi a tsakanin al\u2019ummomin karkara.<\/p>\n<p><strong><em>Usman Mohammed Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al&#8217;umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana. Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5533,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[320,59],"class_list":["post-5531","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-ambaliya","tag-jigawa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250803-WA0039.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5531","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5531"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5531\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5534,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5531\/revisions\/5534"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5533"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5531"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5531"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5531"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}