{"id":5513,"date":"2025-08-01T15:38:53","date_gmt":"2025-08-01T15:38:53","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5513"},"modified":"2025-08-01T15:38:53","modified_gmt":"2025-08-01T15:38:53","slug":"nbrda-za-ta-hada-gwiwa-da-kirct-domin-habaka-magunguna-da-yaki-da-cututtuka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/nbrda-za-ta-hada-gwiwa-da-kirct-domin-habaka-magunguna-da-yaki-da-cututtuka\/","title":{"rendered":"NBRDA Za Ta Hada Gwiwa Da KIRCT Domin Habaka Magunguna Da Yaki Da Cututtuka"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases).<\/p>\n<p>Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ya kai hedikwatar KIRCT\u00a0 da ke Kano.<\/p>\n<p>Farfesa Mustapha ya ce ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa tsakanin NBRDA da KIRCT domin magance kalubalen da kasa ke fuskanta ta hanyar binciken zamani.<\/p>\n<p>\u201c<em>A matsayina na shugaba a wata muhimmiyar hukuma da ke da alhakin bincike da ci gaban fasahar halittu a fannonin abinci da noma, lafiya, masana\u2019antu da muhalli, muna da cikakken shiri na tallafa wa KIRCT don cimma manufofinta<\/em>.\u201d<\/p>\n<p>Ya yaba da kayan aiki na zamani da ke cibiyar, yana mai cewa suna da babban amfani wajen kawo sakamako mai tasiri da kuma daga martabar Najeriya a fagen binciken kimiyya na duniya.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Daraktan Janar na KIRCT, Farfesa Hamisu Salihu, ya bayyana cewa cibiyar na mai da hankali kan muhimman fannoni guda uku da suka hada da taimaka wa manyan masu bincike daga Jami\u2019ar Bayero ta Kano da Jami\u2019ar Northwest, da\u00a0 horar da sabbin masana bincike, wato masu tasuwa, da kuma kaddamar da wani shirin gwaji na horas da dalibai biyar mafi hazaka daga ajin karshe na sakandare kan ilimin fasahar halittu kafin su shiga jami\u2019a.<\/p>\n<p>Farfesa Hamisu ya jaddada muhimmancin kafafen watsa labarai da kuma Ma\u2019aikatar Lafiya ta Jihar Kano wajen bunkasa fasahar halittu da inganta tattalin arzikin ilimi.<\/p>\n<p>Ya kuma sake nanata kudurin KIRCT na ci gaba da gudanar da bincike mai tasiri da amfani.<\/p>\n<p>Wakiliyar Rediyon Najeriya ta ruwaito\u00a0 cewa an kafa Kano Independent Research Centre Trust(KIRCT) ne domin gudanar da bincike kan kiwon lafiya da cututtuka masu yaduwa da wadanda ba sa yaduwa, masu matukar muhimmanci ga lafiyar jama&#8217;a a Najeriya da ma fadin nahiyar Afirka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyar ta na hadin gwiwa da Cibiyar Binciken Cututtuka ta Jihar Kano(KIRCT) a fannonin bincike, samar da rigakafi, habaka magunguna da kuma yaki da cututtuka masu nasaba da zafi (tropical diseases). Darakta Janar na Hukumar Binciken Harkokin Halittu ta Kasa (NBRDA), Farfesa Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5514,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[7,3,1,11,4],"tags":[39,1404,1403],"class_list":["post-5513","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fasaha","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kano","tag-kirct","tag-nbrda"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/08\/IMG-20250801-WA0022.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5513","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5513"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5513\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5515,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5513\/revisions\/5515"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5514"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5513"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5513"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5513"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}