{"id":5343,"date":"2025-07-28T14:29:34","date_gmt":"2025-07-28T14:29:34","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5343"},"modified":"2025-07-28T14:29:34","modified_gmt":"2025-07-28T14:29:34","slug":"majalisar-dokokin-jihar-kano-ta-bukaci-a-kara-inganta-aikin-titin-gabasawa","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/majalisar-dokokin-jihar-kano-ta-bukaci-a-kara-inganta-aikin-titin-gabasawa\/","title":{"rendered":"Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Bukaci A Kara Inganta Aikin Titin Gabasawa"},"content":{"rendered":"<p>Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa.<\/p>\n<p>Wannan mataki ya biyo bayan kar\u0253ar rahoton da Kwamitin\u00a0 Majalisar kan Harkokin Jin\u0199ai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta Gabasawa.<\/p>\n<p>Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana wasu muhimman shawarwari da suka hada da: Umurtar kamfanin da ke aikin gina hanyar da ya fa\u0257a\u0257a magudanar ruwa a yankin da abin ya shafa da kuma gaggauta kai agajin gaggawa ga wa\u0257anda ambaliyar ta shafa.<\/p>\n<p>Sauran shawarwarin sun ha\u0257a da tura tawagar \u0199wararru daga ma\u2019aikatun ayyuka da muhalli na jihar don gudanar da bincike da bayar da shawarwarin fasaha.<\/p>\n<p>Bayan nazari da tattaunawa mai zurfi, majalisar ta amince da rahoton baki \u0257aya tare da kiran gwamnatin jihar da ta gaggauta \u0257aukar mataki domin rage tasirin ambaliya a Zakirai.<\/p>\n<p>A wani sabon lamari kuma, majalisar ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta gaggauta sake gina hanyar da ke ha\u0257a Kwanar \u2018Yan Mota zuwa Kwanar Bakin Zuwo zuwa Jakara, zuwa Kwanar Gabari a cikin karamar hukumar birnin Kano.<\/p>\n<p>Wanda ya gabatar da kudirin, Honarabul Aliyu Yusuf Daneji, mai wakiltar mazabar Kano Municipal, ya jaddada cewa hanyar, musamman a kusa da kasuwar Kurmi, tana cikin matsanancin hali wanda ke kawo cikas ga zirga-zirga da kuma lalata harkokin kasuwanci.<\/p>\n<p>Haka kuma, Alhaji Abdullahi Yahaya, mai wakiltar mazabar Gezawa, ya gabatar da kudiri na bu\u0199atar gina titin kwalta daga Jogana zuwa Matallawa, Yamadi Charo da Daraudau.<\/p>\n<p>Ya ce hanyar ba ta dadin bi a lokacin damina, inda al\u2019ummar yankin ke \u0257aukar matakin kansu ta hanyar cike ramuka da yashi da itace.<\/p>\n<p>Kudirin ya samu goyon bayan Jagoran Masu Rinji a Majalisar, Alhaji Zakariyya Abdullahi Nuhu, tare da cikakken goyon bayan \u2018yan majalisar baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Sauran kudirori da aka amince da su a zaman sun ha\u0257a da: Gina titi daga Dalawada zuwa Gazobi a karamar hukumar Tudun Wada da kuma sake gina hanyar Fanisau a Ungogo.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Daga Khadijah Aliyu<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa. Wannan mataki ya biyo bayan kar\u0253ar rahoton da Kwamitin\u00a0 Majalisar kan Harkokin Jin\u0199ai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5344,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[39,211],"class_list":["post-5343","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-kano","tag-majalisa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/KANO-ASSEMBLY.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5343","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5343"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5343\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5345,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5343\/revisions\/5345"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5344"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5343"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5343"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5343"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}