{"id":5316,"date":"2025-07-26T21:01:21","date_gmt":"2025-07-26T21:01:21","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5316"},"modified":"2025-07-26T21:05:50","modified_gmt":"2025-07-26T21:05:50","slug":"an-fara-zaman-jin-raayoyin-jamaa-kan-sauya-kundin-tsarin-mulki-a-kano","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/an-fara-zaman-jin-raayoyin-jamaa-kan-sauya-kundin-tsarin-mulki-a-kano\/","title":{"rendered":"An Fara Zaman Jin Ra\u2019ayoyin Jama\u2019a Kan Sauya Kundin Tsarin Mulki A Kano"},"content":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra\u2019ayoyin jama\u2019a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano.<\/p>\n<p>Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa:<em> \u201cIna alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra\u2019ayoyin jama\u2019a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya<\/em>.\u201d<\/p>\n<p>Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar \u0198asa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke bu\u0199atar \u0199arin matakin doka domin warware su. Cikin batutuwan da za a mayar da hankali a kansu akwai: Sauye-sauyen harkar za\u0253e, gyara a fannin shari\u2019a, gyaran kundin tsarin mulki, da gudanar da shari\u2019u da tsare-tsarensu.<\/p>\n<p>Sauran muhimman batutuwa sun ha\u0257a da:Inganta \u2018yancin \u0257an adam, tabbatar da shigar mata a harkokin shugabanci, raba iko da ha\u0253aka ci gaban \u0199ananan hukumomi, batutuwan tsaro da tsarin aikin \u2018yan sanda, da sauransu.<\/p>\n<p>Sanata Barau ya bu\u0199aci dukkan masu ruwa da tsaki da su ba da ra\u2019ayoyi da shawarwari, yana mai cewa: \u201c<em>Mun bu\u0257e \u0199ofofinmu ga dukkan ra\u2019ayoyi. Kwamitin ya kuduri aniyar sauraron dukkanin bangarori yadda yakamata<\/em>.\u201d In ji shi.<\/p>\n<p>Ya jaddada cewa shiga cikin irin wannan tsari na jama\u2019a muhimmin al\u2019amari ne ga makomar \u0199asa.<\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Shugaban Ma\u2019aikatan Gwamnatin Jiha, Dr. Wali Sani, ya wakilta, ya jaddada bukatar ha\u0257in kai, adalci da daidaito. A cewarsa: \u201c<em>ya zama mu yi ayyukan da za su ha\u0257a \u0199asa, su inganta adalci da daidaito, su kuma ha\u0253aka ci gaba da bun\u0199asa tattalin arzikin \u0199asa gaba \u0257aya.\u201d<\/em><\/p>\n<p><strong><em>Abdullahi Jalaluddeen<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra\u2019ayoyin jama\u2019a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: \u201cIna alfahari da zuwanku wannan zama [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":0,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[39,1379],"class_list":["post-5316","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-labarai","tag-kano","tag-raayoyin-jamaa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5316","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5316"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5316\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5318,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5316\/revisions\/5318"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5316"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5316"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5316"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}