{"id":5254,"date":"2025-07-23T14:33:24","date_gmt":"2025-07-23T14:33:24","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5254"},"modified":"2025-07-23T14:33:24","modified_gmt":"2025-07-23T14:33:24","slug":"gwamna-namadi-ya-amince-da-nadin-sabbin-sakatarori-guda-takwas","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamna-namadi-ya-amince-da-nadin-sabbin-sakatarori-guda-takwas\/","title":{"rendered":"Gwamna Namadi Ya Amince Da Nadin Sabbin Sakatarori Guda Takwas"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan\u00a0 sakatarori\u00a0 guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma&#8217;aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.<\/p>\n<p>Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma\u2019aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga cikin sabbin sauye-sauyen akwai Sagir Muhammad Sani daga Ma\u2019aikatar Ilimin Firamare zuwa Ma\u2019aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki, da kuma Muhammad Yusha\u2019u daga Ma\u2019aikatar Tsare-tsare da Tattalin Arziki zuwa Ma\u2019aikatar Harkokin Kananan Hukumomi.<\/p>\n<p>Sai Lawan Muhammad Haruna daga Ma\u2019aikatar Ilimi Mai Zurfi zuwa Hukumar Kula da Ayyukan Kananan Hukumomi, da kuma Injiniya Musa Alhassan Arobade daga Ma\u2019aikatar Wuta da Makamashi zuwa Hukumar Bun\u0199asa Ma&#8217;aikata da Horaswa, wadda ke \u0199ar\u0199ashin ofishin Shugaban Ma\u2019aikata na Jiha.<\/p>\n<p>Alhaji Muhammad Dagaceri ya bayyana cewa, sabbin sakatarorin da aka nada su ne Garba D. Muhammad zuwa Ma\u2019aikatar Ilimi Mai Zurfi, da Kimiyya da Fasaha, da Fatima Aliyu Hadejia zuwa Hukumar Albashi da Fansho \u0199ar\u0199ashin ofishin Shugaban Ma\u2019aikata.<\/p>\n<p>Sauran sun ha\u0257a da Baffa Abubakar wanda aka tura zuwa Ma\u2019aikatar Ilimin Firamare, sai Bello Datti zuwa Sashen Kula da Harkokin Musamman\/Al\u2019amuran Majalisar Zartarwa \u0199ar\u0199ashin ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, da Ibrahim Hassan zuwa Ma\u2019aikatar Ku\u0257i, da kuma Nasiru Haruna zuwa Ma\u2019aikatar Wuta da Makamashi, sai Umar Isah zuwa Hukumar Kula da Ma\u2019aikata, yayin da Mahmud Isah Ringim aka tura shi zuwa Ma\u2019aikatar Kasuwanci da Masana\u2019antu.<\/p>\n<p>Shugaban Ma\u2019aikatan ya \u0199ara da cewa, wannan sauyin zai fara aiki ne nan take.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Usman Muhammad Zaria<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin sabbin manyan\u00a0 sakatarori\u00a0 guda takwas, da kuma mayar da wasu hudu zuwa wasu ma&#8217;aikatu, da hukumomi da sassan gwamnati daban-daban. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma\u2019aikatan jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya fitar a Dutse, inda ya bayyana cewa daga [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":4811,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[59,1207],"class_list":["post-5254","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-jigawa","tag-sakatarori"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/06\/namadi-Umar.webp","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5254"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5255,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5254\/revisions\/5255"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4811"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5254"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5254"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5254"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}