{"id":5251,"date":"2025-07-23T14:01:18","date_gmt":"2025-07-23T14:01:18","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5251"},"modified":"2025-07-23T14:01:18","modified_gmt":"2025-07-23T14:01:18","slug":"unicef-ya-bukaci-jihar-kano-ta-bai-wa-yara-muhimmanci-a-kasafin-kudi","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/unicef-ya-bukaci-jihar-kano-ta-bai-wa-yara-muhimmanci-a-kasafin-kudi\/","title":{"rendered":"UNICEF Ya Bukaci Jihar Kano Ta Bai Wa Yara Muhimmanci A Kasafin Kudi"},"content":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta \u0199ara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin ku\u0257i da ya danganci makomar yara.<\/p>\n<p>Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Muhammad Farah, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da \u2018yan jarida kan kasafin ku\u0257i mai la\u2019akari da bukatun yara, inda ya gabatar da wasu alkalumma masu tayar da hankali dangane da rayuwar yara a jihar.<\/p>\n<p>Farah ya ce jihar Kano na da yara fiye da miliyan 6 da rabi da ke \u0199asa da shekaru 18, wadanda da dama daga cikinsu na fuskantar matsaloli masu tsanani kamar mace-macen yara, \u0199arancin abinci mai gina jiki, da kuma rashin samun ingantaccen ilimi da kiwon lafiya.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa, bisa ga rahoton MICS na 2021, yara 143,000 na mutuwa kafin su kai shekara biyar, yayin da kusan yara miliyan 2 da 900,000 ba su da cikakken rigakafi, sannan fiye da yara miliyan 4 na rayuwa cikin talauci.<\/p>\n<p>Haka kuma, sama da yara miliyan 2 300,000 da suka kai shekarun makaranta suna zaune a gida ba tare da samun ilimi ba, wani hali da ya ce ya zama wajibi a sauya shi ta hanyar karfafa kasafin ku\u0257i na kula da yara.<\/p>\n<p>Ya ce duk da wasu sauye-sauye da ake yi, fannin walwalar al\u2019umma a Kano har yanzu na samun \u0199arancin kudi, inda ya zargi sauyin kasafi da rashin daidaito a fannonin lafiya, ilimi da kare hakkin yara da janyo cikas ga cigaba.<\/p>\n<p>Farah ya bayyana kasafin ku\u0257i mai kula da yara a matsayin wata dabara mai mahimmanci, fiye da ware ku\u0257i kawai ga makarantu da asibitoci.<\/p>\n<p>A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Muhammad Bello Butu Butu, ya tabbatar da kudurin majalisar na tabbatar da cikakken aiwatar da kasafin ku\u0257i ga ma\u2019aikatu da hukumomi.<\/p>\n<p>Sai dai ya soki wasu shugabannin ma\u2019aikatu da hukumomi da rashin kokarin kar\u0253ar ku\u0257a\u0257en da aka ware musu da kuma gazawar aiwatar da su, duk da kokarin bangaren zartarwa wajen sakin kudin. Ya bayyana cewa kimanin kashi 35% na kasafin ku\u0257in jihar na zuwa fannin lafiya ne da ilimi.<\/p>\n<p>Masu ruwa da tsaki da suka halarci taron, ciki har da \u2018yan jarida, kungiyoyin farar hula, da ma\u2019aikatun gwamnati, sun yi kira ga gwamnatin Kano da ta tabbatar da kasafin ku\u0257i mai la\u2019akari da yara, ta \u0199ara yawan ku\u0257a\u0257en da ake warewa shirye-shiryen kula da yara, tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana a wajen aiwatar da kasafin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Khadijah Aliyu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Asusun Kula da Yara na Majalisar \u018ainkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta \u0199ara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin ku\u0257i da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5252,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,4],"tags":[39,704],"class_list":["post-5251","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kano","tag-unicef"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250723-WA0001.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5251","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5251"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5251\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5253,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5251\/revisions\/5253"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5252"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5251"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5251"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5251"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}