{"id":5192,"date":"2025-07-21T12:58:26","date_gmt":"2025-07-21T12:58:26","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5192"},"modified":"2025-07-21T12:58:26","modified_gmt":"2025-07-21T12:58:26","slug":"libya-ta-tasa-keyar-ba%c6%99in-haure-yan-kasar-sudan-700-zuwa-kasarsu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/libya-ta-tasa-keyar-ba%c6%99in-haure-yan-kasar-sudan-700-zuwa-kasarsu\/","title":{"rendered":"Libya Ta Tasa Keyar Ba\u0199in Haure Yan Kasar Sudan 700 Zuwa Kasarsu"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan ba\u0199in haure &#8216;yan \u0199asar Sudan 700 zuwa \u0199asarsu da ya\u0199i ya \u0257ai\u0257aita, A cewar mahukuntan, wa\u0257annan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa ya\u0199i da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai.<\/p>\n<p>A cewar hu\u0199umar kula da ba\u0199in haure, an kori mutane 700 daga Libya da aka kama a tsakiya da kudu maso gabashin \u0199asar, inda aka tura su zuwa Sudan a ranar Juma&#8217;ar da ta gabata ta \u0199asa.<\/p>\n<p>Bayanin ya nuna cewa wasu daga cikin wa\u0257anda aka korar na \u0257auke da cututtuka masu ya\u0257uwa kamar su hepatitis da cuta mai karya garkuwar jiki, wasu kuma an tura su ne saboda laifuffuka ko kuma dalilan tsaro.<\/p>\n<p>Korar ta zo ne a lokacin da mahu\u0199untan ke ci gaba da ya\u0199i da safarar mutane a gabashin Libya, wanda ke \u0199ar\u0199ashin ikon kwamandan sojoji Khalifa Hiftar.<\/p>\n<p>A makon da ya gabata, masu tsaron ga\u0253ar teku a gabashin Libya sun kame wani jirgin ruwa da ke \u0257auke da ba\u0199in haure 80 da ke neman zuwa \u0199asashen \u0199etare, a gabashin birnin Tobruk.<\/p>\n<p>Ya\u0199in da hukumomin ke yi sun ha\u0257a da kai hare-hare kan wuraren da ake safarar mutane a gabashi da kudancin Libya. A farkon wannan watan, an \u0199wato ba\u0199in haure &#8216;yan Sudan 104, ciki har da mata da yara, da aka tsare a gidan da ake tara mutane da ake fataucin su a birnin Ajdabiya, mai nisan kilomita 800 daga babban birnin Tripoli, a cewar \u01b4an sa kai na yankin.<\/p>\n<p>Libya ta zama hanyar wucewa ga mutanen da ke guje wa ya\u0199i da talauci a yankunan gabas ta tsakiya da Afirka, inda suke neman rayuwa mai kyau a Turai.<\/p>\n<p>Masu safarar mutane sun ci gajiyar rashin kwanciyar hankali a Libya tsawon shekaru goma, inda suke shigar da ba\u0199in haure ta iyakokin \u0199asar da suka ha\u0257a da \u0199asashen Chadi da Nijar da Sudan da Masar da Aljeriya da kuma Tunisiya.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Libya ta tasa keya daruruwan ba\u0199in haure &#8216;yan \u0199asar Sudan 700 zuwa \u0199asarsu da ya\u0199i ya \u0257ai\u0257aita, A cewar mahukuntan, wa\u0257annan mutanen sun yi hijira zuwa Libya ne domin gujewa ya\u0199i da talauci, inda suke neman hanyar tsallakawa zuwa Turai. A cewar hu\u0199umar kula da ba\u0199in haure, an kori mutane 700 daga Libya da [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5195,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,12],"tags":[769,1354,151],"class_list":["post-5192","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-ketare","tag-bakin-haure","tag-libya","tag-sudan"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/F2E2EC57-72C1-4B69-BB02-FAAFB52765A5.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5192","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5192"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5192\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5196,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5192\/revisions\/5196"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5195"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5192"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5192"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5192"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}