{"id":518,"date":"2024-03-20T04:12:44","date_gmt":"2024-03-20T04:12:44","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=518"},"modified":"2024-03-20T06:55:18","modified_gmt":"2024-03-20T06:55:18","slug":"yajin-aikin-nasuu-da-ssanu-ya-gurgunta-harkikin-karatu-a-jamioin-nujeriya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/yajin-aikin-nasuu-da-ssanu-ya-gurgunta-harkikin-karatu-a-jamioin-nujeriya\/","title":{"rendered":"Yajin Aikin NASUU da SSANU Ya Gurgunta harkikin Karatu a Jami&#8217;o&#8217;in Nujeriya"},"content":{"rendered":"<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-519\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003-300x135.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"135\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003-300x135.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003-1024x461.jpg 1024w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003-768x346.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003.jpg 1280w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<blockquote><p>Yajin aikin da Kungiyar ma&#8217;aikatan Jami&#8217;o&#8217;i ta kasa da suka hada da NASUU da SSANU suka fara gudanar wa ya gurgunta harkokin karatu a Jami&#8217;ar Ahmadu Bello dake Zaria.<\/p><\/blockquote>\n<p>Kungiyoyin ma&#8217;aikatan sun fara yajin aikin ne na kwanaki bakwai a matsayin na gargadi.<\/p>\n<p>Wakilin Radio Najeriya ya bayyana cewa shugabannin Kungiyar sun rufe duk kofofin shiga Jami&#8217;ar inda dalibai da malamai na shiga harabar Jami&#8217;ar ce kawai ta hanyar taka sayyada.<\/p>\n<p>Haka kuma kungiyoyin sun rufe duk wasu ayyuka a harabar dakunan kwanan dalibai da wuraren samar da ruwan sha da wutar lantarki da dakunan karatu,yayin da sauran ma&#8217;aikatan duk suka yi zaman su gida domin bin umurnin kungiyoyin.<\/p>\n<p>Da yake zantawa da Radio Najeriya yayin wani tattaki da Yayan kungiyoyin suka gudanar daga ofishin Shugaban jami&#8217;ar zuwa babbar kofar shiga Jami&#8217;ar, shugaban gamayyar kungiyoyin, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar manyan ma&#8217;aikatan Jami&#8217;ar Ahmadu Bello, kwamared Mohammed Yunusa ya ce kungiyoyin sun hana gudanar da aiyukan Jami&#8217;ar ne tun ranar Litinin da aka fara yajin aikin kamar yadda uwar kungiyar ta kasa ta basu umurni.<\/p>\n<p>Shugaban ya ce sun fara yajin aikin ne sakamakon rukon sakainar kashi da nuna bambanci da gwamnatin tarayya ke yi masu wajen biyan albashi da kuma gazawar gwamnati wajen cika alkawuran da ta yi a tsakanin su.<\/p>\n<p>Kwamared Yunusa ya ce shugaban kasa ya bada umurnin a biya su amma wasu Jami&#8217;ai sun ki biya.<\/p>\n<p>A cewar sa,Jami&#8217;an sun ki biyan su ne kasancewar basa daukar yayan kungiyoyin da muhimmanci wajen tafiyar da harkokin Jami&#8217;a,kasancewar kungiyar malaman Jami&#8217;o&#8217;i kawai suke ba muhimmanci.<\/p>\n<p>Shugaban gamayyar kungiyoyin ya tunasar da gwamnati game da halin da harabar Jami&#8217;o&#8217;in za su kasance idan babu ruwa da wuta da kuma dakunan karatu da na bincike idan suka kasance a rufe.<\/p>\n<p>Kwamared Mohammed Yunusa ya ce yajin aikin nasu ya yi nasara kasancewar yayan kungiyoyin biyu sun bi umurnin uwar kungiyar ta kasa.<\/p>\n<p>Haliru Hamza<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Yajin aikin da Kungiyar ma&#8217;aikatan Jami&#8217;o&#8217;i ta kasa da suka hada da NASUU da SSANU suka fara gudanar wa ya gurgunta harkokin karatu a Jami&#8217;ar Ahmadu Bello dake Zaria. Kungiyoyin ma&#8217;aikatan sun fara yajin aikin ne na kwanaki bakwai a matsayin na gargadi. Wakilin Radio Najeriya ya bayyana cewa shugabannin Kungiyar sun rufe duk kofofin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":519,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,4,10,2,9,8],"tags":[17],"class_list":["post-518","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","category-noma","category-siyasa","category-tattalin-arziki","category-tsaro","tag-nlc"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/03\/IMG-20240320-WA0003.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/518","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=518"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/518\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":522,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/518\/revisions\/522"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/519"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=518"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=518"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=518"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}