{"id":5161,"date":"2025-07-20T16:29:43","date_gmt":"2025-07-20T16:29:43","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5161"},"modified":"2025-07-20T16:29:43","modified_gmt":"2025-07-20T16:29:43","slug":"iyalan-muhammadu-buhari-sun-bayyana-godiyarsu-ga-yan-najeriya-da-sauran-kasashen-duniya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/iyalan-muhammadu-buhari-sun-bayyana-godiyarsu-ga-yan-najeriya-da-sauran-kasashen-duniya\/","title":{"rendered":"Iyalan Muhammadu Buhari Sun Bayyana  Godiyarsu Ga &#8216;Yan Najeriya Da Sauran Kasashen Duniya"},"content":{"rendered":"<p>Iyalan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya ta musamman ga \u2018yan Najeriya da al\u2019ummomin kasashen duniya bisa goyon baya da nuna alhini lokacin rasuwar marigayin.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu a madadin iyalan, ta bakin Malam Mamman Daura, sun mika godiya ta musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu, bisa kulawar da suka nuna kafin, da kuma bayan rasuwar tsohon shugaban kasar.<\/p>\n<p>\u201c<em>Irin ziyarce-ziyarcen da aka kai, sa\u0199onnin jaje, da kuma yanke hukuncin ayyana hutu da kuma canza sunan Jami\u2019ar Maiduguri zuwa Buhari, duk sun kasance alamu ne na tausayawa da suka sanya mana kwarin gwiwa<\/em> \u201d in ji iyalan.<\/p>\n<p>Hakazalika sun jinjinawa\u00a0 mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, wanda ya yi tafiya zuwa Birtaniya sannan ya kai ziyara Daura tare da wasu ministoci a lokacin makokin. \u201c<em>Hakan ya karfafa mana gwiwa wajen fuskantar wannan babban rashi<\/em>,\u201d in ji sanarwar.<\/p>\n<p>Iyalan sun kuma gode wa manyan shugabannin duniya, ciki har da Sarki Charles III na Birtaniya, Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ant\u00f3nio Guterres, da mataimakiyar\u00a0 Amina Mohammed, Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da shugabannin kasashen ECOWAS bisa jajentawa, wasiku, da ziyarar gaisuwa ko kiran waya.<\/p>\n<p>Sun kuma yaba da ziyarce-ziyarce da sakonni daga shugabannin Najeriya na yanzu da na baya, ciki har da tsofaffin shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, tsofaffin mataimakan shugaban kasa Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Yemi Osinbajo, da Ambasada Babagana Kingibe.<\/p>\n<p>Gwamnonin jihohi daban-daban musamman gwamnan jihar Katsina Dr. Dikko Umar Radda, gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, da tsohon gwamnan jihar Anambra Dr. Peter Obi, duk sun samu yabo bisa irin tausayin da suka nuna.<\/p>\n<p>Sanarwar ta kara da godiya ga shugabannin Majalisar Tarayya ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin, da sauran \u2018yan majalisa na matakin kasa da jihohi.<\/p>\n<p><em>&#8220;Har ila yau muna jinjina ga Sarakuna daga sassa daban-daban na Najeriya, ciki har da Nai Alfarma Sarkin Musulmai, Shehun Borno, da sarakunan Gwandu, Katsina, da Daura.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Iyalan Buhari sun kuma gode wa shugabannin addinai da na al\u2019umma, kungiyoyin matasa, mata, \u2018yan siyasa, ma\u2019aikata, jami\u2019an tsaro, da kafafen watsa labarai da suka shiga cikin al\u2019amuran makokin.<\/p>\n<p>Sai kuma manyan \u2018yan kasuwa da suka hada da Aliko Dangote, Abdul Samad Rabiu, Muhammadu Indimi, Dahiru Mangal, Kola Adesina, wadanda su ma sun kasance da iyalan marigayin yayin jimamin rashinsa.<\/p>\n<p>Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2015 zuwa 2023, ya rasu a Birtaniya a farkon wannan wata. An binne shi a mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><em><strong>Bello Wakili<\/strong><\/em><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Iyalan tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya ta musamman ga \u2018yan Najeriya da al\u2019ummomin kasashen duniya bisa goyon baya da nuna alhini lokacin rasuwar marigayin. A cikin wata sanarwa da Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu a madadin iyalan, ta bakin Malam Mamman Daura, sun mika godiya ta musamman ga shugaban kasa [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5081,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11],"tags":[1351,96],"class_list":["post-5161","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","tag-godiya","tag-muhammadu-buhari"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/thumbs_b_c_d30add476ac649f70e9f6c4a759d03c5.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5161","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5161"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5161\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5162,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5161\/revisions\/5162"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5081"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5161"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5161"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5161"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}