{"id":5154,"date":"2025-07-20T12:14:50","date_gmt":"2025-07-20T12:14:50","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5154"},"modified":"2025-07-20T16:03:34","modified_gmt":"2025-07-20T16:03:34","slug":"jihar-kwara-ta-samar-da-rijiyar-burtsatse-mai-amfani-da-hasken-rana-ga-makiyaya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/jihar-kwara-ta-samar-da-rijiyar-burtsatse-mai-amfani-da-hasken-rana-ga-makiyaya\/","title":{"rendered":"Jihar Kwara Ta Samar Da Rijiyar Burtsatse Mai Amfani Da Hasken Rana Ga Makiyaya"},"content":{"rendered":"<p>Shirin Taimakawa da \u0198arfafa Samar da Amfanin Dabbobi na Jihar Kwara (L-PRES) ya mika sabon aikin rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana ga al\u2019ummar Fulani da ke \u0199aramar hukumar Asa a Jihar Kwara.<\/p>\n<p>Yayin bikin mika aikin, jami\u2019in kula da shirin na L-PRES a Jihar, Mista Olusoji Oyawoye, ya bayyana cewa aikin yana cikin kokarin gwamnatin jihar na rage rikici tsakanin manoma da makiyaya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Wacce ta wakilce shi, jami\u2019ar kula da walwalar jama\u2019a ta shirin, Hajiya Folake Iseyemi, ta ce wannan yun\u0199uri zai taimaka wajen \u0199arfafa juriyar makiyaya\u00a0 dangane da sauyin yanayi da ake fuskanta,\u00a0 da kuma \u0199ara yawan dabbobin da ake sanarwa.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa aikin ya yi daidai da babban burin ci gaba na shirin L-PRES, yana mai cewa an kafa wani kwamiti mai mutum biyar daga cikin al\u2019umma da ke da alhakin tabbatar da dorewar aikin a matakin \u0199auyuka.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-5157\" src=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250720-WA0009-300x226.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"226\" srcset=\"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250720-WA0009-300x226.jpg 300w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250720-WA0009-768x578.jpg 768w, https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250720-WA0009.jpg 1020w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>Oyawoye ya \u0199ara da cewa kwamitin tare da ofishin da ke da alhakin jagorantar shirin zai gudanar da ayyukan da za su \u0199arfafa dangantaka tsakanin manoma da makiyaya, hana rikice-rikice, da kuma samar zaman lafiya tsakanin al\u2019ummomi daban-daban a yankin.<\/p>\n<p>A jawabinsa a madadin al\u2019ummar Fulani, Jowuron Labintan, Alhaji Ibrahim Hamadu, ya gode wa gwamnatin Jihar Kwara, Shirin L-PRES da sauran abokan hul\u0257a bisa wannan karamcin.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa aikin zai rage musu yawan \u0199aura wajen neman ruwa, tare da dakile matsalolin rikici tsakanin manoma da makiyaya a yankin da kuma cikin jihar baki \u0257aya.<\/p>\n<p>Alhaji Hamadu ya kuma ro\u0199i \u0199arin ayyukan da za su rage wahalhalun da makiyaya ke fuskanta, domin bunkasa kiwo da kuma \u0199ara wadatar abinci a \u0199asar.<\/p>\n<p>A yayin bikin, an raba ababen da za su taimakawa makiyayan wajen kiwo, da suka hada da gishirin dabbobi da sauransu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><b><em>Ali Muhammad Rabi&#8217;u<\/em>\u00a0<\/b><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shirin Taimakawa da \u0198arfafa Samar da Amfanin Dabbobi na Jihar Kwara (L-PRES) ya mika sabon aikin rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana ga al\u2019ummar Fulani da ke \u0199aramar hukumar Asa a Jihar Kwara. Yayin bikin mika aikin, jami\u2019in kula da shirin na L-PRES a Jihar, Mista Olusoji Oyawoye, ya bayyana cewa aikin yana cikin [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":5158,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[5,1,11,10,8],"tags":[175,1350,1296],"class_list":["post-5154","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-kasuwanci","category-labarai","category-labaran-gida","category-noma","category-tsaro","tag-kwara","tag-makiyaya","tag-rijiya"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250720-WA0008.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5154","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5154"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5154\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5160,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5154\/revisions\/5160"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5158"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5154"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5154"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5154"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}