{"id":5103,"date":"2025-07-16T15:07:08","date_gmt":"2025-07-16T15:07:08","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5103"},"modified":"2025-07-16T15:07:08","modified_gmt":"2025-07-16T15:07:08","slug":"gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-bincike-kan-mutuwar-dalibai-biyu-a-makaranta","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/gwamnatin-kano-ta-kaddamar-da-bincike-kan-mutuwar-dalibai-biyu-a-makaranta\/","title":{"rendered":"Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Bincike Kan Mutuwar Dalibai Biyu A Makaranta"},"content":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan mutuwar ban mamaki ta wasu dalibai biyu a Kwalejin Sakandaren Gwamnati ta kwana da ke Bichi, wato Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa.<\/p>\n<p>Rahotanni sun ce wasu daliban makarantar ne suka kai musu hari da wani irin l \u0199arfe da ake kira \u201cGwale-Gwale\u201d.<\/p>\n<p>Lamarin ya tayar da \u0199ura inda al&#8217;umma a fadin jihar suka nemi a tabbatar da adalci game da lamarin.<\/p>\n<p>Yayin da yake magana da manema labarai a madadin Kwamishinan Ilimi Dr. Ali Haruna Makoda, Babban Sakataren Ma\u2019aikatar Ilimi, Alhaji Bashir Baffa Muhammad, ya bayyana cewa gwamnati ta \u0257auki lamarin da muhimmanci kuma ba za ta yi sakaci ba wajen tabbatar da adalci.<\/p>\n<p><em>\u201cGwamnatin Jihar Kano za ta gudanar da bincike busa gaskiya, da adalci. Mun sha alwashin ganin an tabbatar da adalci ga dukkan wadanda lamarin ya shafa.\u201d Inji shi\u00a0<\/em><\/p>\n<p>Ya ja hankalin dalibai da su guji \u0257aukar doka a hannunsu, su ri\u0199a kai koke-kokensu ga mahukuntan makaranta.<\/p>\n<p>Babban Sakataren ya kuma mi\u0199a ta\u2019aziyyar gwamnati ga iyalan mamatan, tare da addu\u2019ar samun rahama garesu.<\/p>\n<p>Shugaban Sashen Makarantun Sakandare na Hukumar Gudanar da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Malam Abbas Abdullahi, ya bayyana matakin da aka \u0257auka a matsayin abin takaici inda ya gargadi dalibai su guji yin amfani da matsayinsu wajen cutar da wasu da kuma aikata tashin hankali.<\/p>\n<p>Wani \u0257an uwa ga \u0257aya daga cikin mamatan, Malam Ibrahim Yusuf Dungurawa, ya bayyana irin radadin da suka shiga bayan samun labarin mutuwar \u0257ansu, tare da ro\u0199on gwamnati da ta tabbatar da adalci.<\/p>\n<p>Haka zalika, mahaifin \u0257aya daga cikin daliban da suka rasu, Malam Idris Garba Tofawa, ya ce sun \u0257auki lamarin a matsayin \u0199addarar Ubangiji, amma ya bukaci hukumomi da su \u0257auki matakin gaggawa don hana maimaituwar irin wannan lamari.<\/p>\n<p>Ya ce: <em>\u201cMuna ro\u0199on a tabbatar da adalci, ba don \u0257anmu ka\u0257ai ba, har ma da lafiyar sauran dalibai gaba \u0257aya.\u201d<\/em><\/p>\n<p>Yayin da ake ci gaba da bincike, Gwamnatin Kano ta sake jaddada kudirinta na kare lafiyar dalibai da kuma tabbatar da doka da oda a dukkan makarantun gwamnati.<\/p>\n<p>Ana sa ran hukumomin tsaro za su ba da goyon baya wajen gudanar da binciken da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Khadijah Aliyu<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da bincike kan mutuwar ban mamaki ta wasu dalibai biyu a Kwalejin Sakandaren Gwamnati ta kwana da ke Bichi, wato Hamza Idris Tofawa da Umar Yusuf Dungurawa. Rahotanni sun ce wasu daliban makarantar ne suka kai musu hari da wani irin l \u0199arfe da ake kira \u201cGwale-Gwale\u201d. Lamarin ya tayar [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":0,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[3,1,11,8],"tags":[354,248,39,410],"class_list":["post-5103","post","type-post","status-publish","format-standard","hentry","category-ilimi","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-bincike","tag-dalibai","tag-kano","tag-kisa"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5103","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5103"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5103\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5104,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5103\/revisions\/5104"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5103"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5103"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5103"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}