{"id":5035,"date":"2025-07-10T17:56:56","date_gmt":"2025-07-10T17:56:56","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=5035"},"modified":"2025-07-10T17:56:56","modified_gmt":"2025-07-10T17:56:56","slug":"efcc-ta-yi-gargadi-kan-damfara-ta-hanyar-ku%c9%97a%c9%97en-intanet-da-zuba-jari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/efcc-ta-yi-gargadi-kan-damfara-ta-hanyar-ku%c9%97a%c9%97en-intanet-da-zuba-jari\/","title":{"rendered":"EFCC Ta Yi Gargadi Kan Damfara Ta Hanyar Ku\u0257a\u0257en Intanet da Zuba Jari"},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A wani \u0253angare na bikin Ranar Ya\u0199i da Cin Hanci ta Afirka, Shugaban<\/p>\n<p>Ya\u0199i da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mr. Ola Olukoyede, ya yi garga\u0257i kan barazanar da ke \u0199ara \u0199amari na damfara ta hanyar ku\u0257a\u0257en zamani da kuma zuba jari na bogi a Najeriya da sauran sassan nahiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mr. Olukoyede ya bayyana hakan ne a yayin bukin ranar ya\u0199i da cin hanci da rashawa ta Afirka a wajen wani taron tattaunawa da aka gudanar a ofishin EFCC na shiyyar Kaduna.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Darakta na riko na shiyyar Kaduna, Bawa Usman Kaltungo wadda ya wakilici Shugaban EFCC ya bayyana cewa nahiyar Afirka na ci gaba da fama da mummunar illar cin hanci da rashawa, musamman ta hanyar fitar da ku\u0257a\u0257en haram zuwa \u0199asashen waje, wanda ya ce ya zama babban cikas ga ci gaban \u0199asashen nahiyar.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cewarsa, Afirka na asarar biliyoyin daloli duk shekara ta hanyar wa\u0257annan haramtattun kudade, inda wanke ku\u0257i ke zama mafi yawa a cikin irin wa\u0257annan laifuka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai kuma, Mr. Olukoyede ya jaddada cewa wata sabuwar barazana da ke \u0199ara yawaita ita ce damfara ta hanyar ku\u0257a\u0257en zamani da na&#8217;ura, kamar su cryptocurrencies da digital tokens.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cKu\u0257a\u0257en zamani da kansu ba laifi ba ne,\u201d in ji shi. \u201cAmma amfani da su ta hanyar yaudara ko rashin bin doka shi ke mayar da su kayan aikata laifi. Abin takaici, masu laifi sun fara amfani da wannan fasaha wajen \u0253oye ku\u0257a\u0257en sata, kaucewa bincike, da kuma aiwatar da shirye-shiryen zuba jari na bogi.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Shugaban EFCC ya ce akwai \u2019yan siyasa da suka fara \u0253oye dukiyar da suka sata ta hanyar cryptocurrency don kaucewa kamun hukumar. A cewarsa, digital wallets na amfani wajen adana ku\u0257a\u0257en da ba a iya bayyana asali, kuma ana amfani da fasahar blockchain wajen biyan ku\u0257in ayyuka marasa tushe.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Sai dai ya jaddada cewa EFCC ta samu ci gaba mai ma\u2019ana wajen bankado da gurfanar da masu aikata irin wa\u0257annan laifuka, inda ya ambaci nasarar da aka samu a bincike da gurfanar da shari\u2019ar damfara ta CBEX.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cDamfara ta ku\u0257a\u0257en zamani da zuba jari ba sabbin \u0199alubale ba ne ga EFCC,\u201d in ji shi. \u201cTa hanyar amfani da basira da horarwa, muna samun nasarori a aikace.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya kuma bayyana damuwa kan yadda damfara ta hanyar zuba jari kamar Ponzi scheme ke yaduwa a fadin Afirka, yana mai cewa masu yaudara na amfani da halin tsananin bukata da rashin sani na masu zuba jari don damfararsu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya ce duk wata hanyar amfani da mutane da nufin amfana da su ta yaudara laifi ce, duk da irin tsarin da aka \u0257aura mata.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Mr. Olukoyede ya yi kira ga jama\u2019a da su guji yanke shawarar zuba jari ba tare da bincike da tabbaci ba, yana mai cewa mafi yawan mutanen da ake damfarawa su ne wa\u0257anda ba sa kai rahoton ababen da ke da alamun damfara har sai da suka rasa ku\u0257a\u0257ensu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cBabu wata damfara ta zuba jari da za ta yi nasara ba tare da sakacin masu zuba jari ba,\u201d in ji shi. \u201cYa zama wajibi a waye kai, a nemi sani, kuma a dauki matakan kariya tun da wuri.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ya sake jaddada cewa EFCC za ta ci gaba da ha\u0257in gwiwa da dukkan masu ruwa da tsaki don hana da kuma binciken irin wa\u0257annan laifuka, yana mai cewa fa\u0257akarwa da wayar da kai na da muhimmanci matu\u0199a.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>\u201cAkwai bu\u0199atar ilimi da fahimta,\u201d ya \u0199ara da cewa. \u201cWannan dandalin tattaunawa wata dama ce ta musayar ra\u2019ayi da fitar da hanyoyin warware wannan matsala. Masana su bayyana wa mahalarta ainihin yadda ku\u0257a\u0257en zamani ke aiki, don a rufe kofar da masu damfara ke amfani da ita.\u201d<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A \u0199arshe, Mista Olukoyede ya bu\u0199aci mahalarta taron da su yi magana cikin gaskiya da fa\u0257akarwa, yana fatan taron zai haifar da fahimta mai zurfi da matakan ha\u0257in gwiwa wajen ya\u0199i da wannan barazana.<\/p>\n<p>COV: Adamu Yusuf<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; A wani \u0253angare na bikin Ranar Ya\u0199i da Cin Hanci ta Afirka, Shugaban Ya\u0199i da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Mr. Ola Olukoyede, ya yi garga\u0257i kan barazanar da ke \u0199ara \u0199amari na damfara ta hanyar ku\u0257a\u0257en zamani da kuma zuba jari na bogi a Najeriya da sauran sassan nahiyar. &nbsp; Mr. Olukoyede ya [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":21,"featured_media":5037,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,8],"tags":[1054,42,568,1127,1338,251,1337,1195],"class_list":["post-5035","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-tsaro","tag-damfara","tag-efcc","tag-gargadi","tag-hanyar","tag-intanet","tag-jari","tag-kuaen","tag-zuba"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/IMG-20250710-WA0027-1.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5035","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/21"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=5035"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5035\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":5038,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/5035\/revisions\/5038"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/5037"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=5035"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=5035"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=5035"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}