{"id":4997,"date":"2025-07-09T08:18:07","date_gmt":"2025-07-09T08:18:07","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4997"},"modified":"2025-07-09T08:18:07","modified_gmt":"2025-07-09T08:18:07","slug":"na-biya-dukkanin-bashin-da-yan-fansho-ke-bin-zamfara-gwamna-lawal","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/na-biya-dukkanin-bashin-da-yan-fansho-ke-bin-zamfara-gwamna-lawal\/","title":{"rendered":"Na Biya Dukkanin Bashin Da &#8216;Yan Fansho Ke Bin Zamfara- gwamna Lawal"},"content":{"rendered":"<p>Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da \u2019Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal<\/p>\n<p>Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin da\u0257insa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka ri\u0199e wa \u2019yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023.<\/p>\n<p>A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan ya \u0199addamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho tare da karbar rahoto daga kwamitocin ha\u0257in gwiwa kan biyan bashin ku\u0257a\u0257en garatuti da aka yi a gidan gwamnati da ke Gusau.<\/p>\n<p>A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, warware tarin bashin ku\u0257a\u0257en guratuti da fansho da aka tara daga shekarar 2011 zuwa 2023 na \u0257aya daga cikin manyan nasarorin da gwamnatin ta samu.<\/p>\n<p>Sanarwar ta \u0199ara da cewa mutane 3,824 da suka yi aiki a \u0199ar\u0199ashin gwamnatin jiha sun samu N7,960,162,598.64, yayin da 4,833 daga \u0199arananan hukumomi aka tantance kuma an biya su N5,983,876,606 a matsayin garatuti. A jimlace, an biya N13,944,039,204.64 a matsayin ku\u0257a\u0257en garatuti.<\/p>\n<p>Gwamna Lawal bayan ya karbi rahoton ya ce gwamnatinsa ta ba da fifiko wajen daidaita biyan ha\u0199\u0199o\u0199in ma\u2019aikatan gwamnati, musamman wa\u0257anda suka yi ritaya bayan shekaru 35 suna aiki kuma suka kai shekaru 60.<\/p>\n<p>\u201cGwamnatinmu ta gaji sama da Naira Biliyan 13 a matsayin bashin ku\u0257a\u0257en garatuti na wa\u0257anda suka yi ritaya daga Jiha da \u0198ananan Hukumomin daga 2011 zuwa 2023, jinkirin ya jawo wahalhalu, kuma wasu da suka yi ritaya sun mutu su na jiran a biya su ha\u0199\u0199in su, Allah ya ji\u0199an su da rahama.<\/p>\n<p>\u201cDon magance wannan rashin adalci, mun kafa kwamitoci guda biyu domin su duba tare da ba da shawarar biyan duk wata garatuti da aka ri\u0199e wa wa\u0257anda suka yi ritaya daga Jiha da \u0198ananan Hukumomi, a lokacin da muka karbi ragamar mulki shekaru biyu da suka wuce, duk da \u0199alubalen tattalin arziki da zamantakewa, mun biya ma\u2019aikatan gwamnati albashin watanni uku tare da biyan su alawus-alawus. Mun kuma daidaita alawus-alawus na al\u0199alai da ma\u2019aikatan shari\u2019a na tsawon shekaru.<\/p>\n<p>\u201cMun daidaita duka wa\u0257annan abubuwa. Lokacin da muka karbi mulki, mafi \u0199arancin albashi a jihar ya kasance Naira 7,000.00 ne kacal, mafi \u0199arancin albashi na N30,000, wanda aka amince da shi a shekarar 2019, gwamnatin da ta shu\u0257e ba ta taba aiwatar da shi ba, saboda sanin nauyin da ya rataya a wuyanmu, mun aiwatar da mafi \u0199arancin albashi na N30,000.00 nan take.<\/p>\n<p>\u201cBayan mun duba tsarin mafi \u0199arancin albashin da ya \u0199aru daga N30,000 zuwa N70,000.00 a watan Yulin 2024, mun aiwatar da sji bayan duk matakan da suka dace, ta yadda a cikin shekaru biyu na mulki, mun \u0199ara mafi \u0199arancin albashi a jihar daga N7,000.00 zuwa N70,000.00.<\/p>\n<p>\u201cBugu da \u0199ari kuma, mun bullo da kuma aiwatar da hanyoyin kyautata wa ma&#8217;aikata a yayin bukukuwan Sallah da kuma \u0199arin garabasar albashin \u0199arshen shekara, wanda aka fi sani da albashin wata na 13 ga duk ma\u2019aikatan gwamnati da masu ri\u0199e da mu\u0199aman gwamnati, ba a taba yin hakan ba a tarihin jihar.<\/p>\n<p>\u201cSakamakon biyan ku\u0257a\u0257en garatuti ya \u0199ara wa ma\u2019aikata kwarin gwiwa tare da dawo da amincewar jama\u2019a kan harkokin mulki, za mu ci gaba da tabbatar da samar da ku\u0257a\u0257en fansho cikin gaggawa, domin yin hakan, gwamnatin jihar a shirye take ta ha\u0257a gwiwa da \u0199ungiyoyin \u2018yan fansho domin tafiya daidai da sauye-sauyen da muka yi.<\/p>\n<p>\u201cYayin da nake samun wannan rahoton, ina so in yaba wa \u0199o\u0199ari da jajircewar \u2018yan kwamitin, wannan ba abu ne mai sau\u0199i ba, ina sane da \u0199alubalen da &#8216;yan kwamitin suka fuskanta a yayin gudanar da aiki, ba yaba da jajircewarsu.<\/p>\n<p>A yayin \u0199addamar da kwamitin aiwatar da ayyukan fansho, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da yin garambawul a harkokin fansho na jiha da \u0199ananan hukumomi.<\/p>\n<p>\u201cGwamnatina ta kafa wani kwamiti da zai duba ayyukan da suka gabata na hukumar fansho a jihar, kwamitin ya kammala aikinsa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a ci gaba, wani bangare na shawarwarin shi ne kafa kwamitin aiwatar da ayyukan fansho.<\/p>\n<p>\u201cDon bin tsarin Ma\u2019aikatar Shari\u2019a, Hukumar Fansho ta Jiha, da duk masu ruwa da tsaki za su duba tare da sabunta dokar fansho ta Jihar Zamfara domin Majalisar Dokokin Jihar ta amince da ita cikin gaggawa.<\/p>\n<p>Aminu Dalhatu\/Gusau<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Na Biya Bashin Garatutin Naira Biliyan 13.6 Da \u2019Yan Fanshon Zamfara Ke Bi Tun 2011, Inji Gwamna Lawal Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin da\u0257insa na biyan bashin Naira Biliyan 13,944,039,204.64 da aka ri\u0199e wa \u2019yan fansho a Zamfara tun daga shekarar 2011 zuwa 2023. A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":17,"featured_media":4998,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1],"tags":[144,115],"class_list":["post-4997","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","tag-bashi","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2025\/07\/d2c46d24-fd2e-452c-8b22-49bc4d1e4597.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4997","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/17"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4997"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4997\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4999,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4997\/revisions\/4999"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/4998"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4997"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4997"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4997"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}