{"id":4923,"date":"2025-07-02T13:03:21","date_gmt":"2025-07-02T13:03:21","guid":{"rendered":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/?p=4923"},"modified":"2025-07-02T13:03:21","modified_gmt":"2025-07-02T13:03:21","slug":"karamar-hukumar-maru-ta-bukaci-a-dauki-matakan-kariya-kan-cutar-kwalaraci","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/karamar-hukumar-maru-ta-bukaci-a-dauki-matakan-kariya-kan-cutar-kwalaraci\/","title":{"rendered":"Karamar Hukumar Maru Ta Bukaci A Dauki Matakan Kariya Kan Cutar Kwalaraci"},"content":{"rendered":"<p>Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al&#8217;ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin.<\/p>\n<p>Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan matakan da hukumar ta dauka domin dakile barkewar cutar ta amai da gudawa a wasu sassan karamar hukumar.<\/p>\n<p>Alhaji Jabaka ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli, musamman wajen tsaftace rijiyoyi da sauran hanyoyin samun ruwan sha, wuraren da ake dafa abinci, da kuma tsaftace muhalli gaba daya, tare da tsaftar jiki wanda ya ce shi ne mabu\u0257in hana yaduwar cutar ta kwalara.<\/p>\n<p>A cewarsa, kwalara cuta ce da za ta iya bulla a ko ina, don haka ya zama wajibi al&#8217;umma su kasance cikin shiri da lura.<\/p>\n<p>Yayin da yake bayani kan halin da aka shiga, ya ce ya gaggauta bayar da umarni ga jami\u2019an lafiya da su dauki wadanda cutar ta shafa zuwa asibitoci domin samun kulawar gaggawa kyauta.<\/p>\n<p>A cewar shugaban karamar hukumar, an samu rahoton mutane sama da 27 da suka kamu da cutar, dukkaninsu kuma sun warke sun koma gida lafiya.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa duk wasu sabbin lamurra na bullar cutar an rika ba da kulawa kyauta ba tare da wata matsala ba.<\/p>\n<p>\u201c<em>Zuwo yanzu, babu rahoton mutuwar kowa sakamakon cutar<\/em>,\u201d in ji shi.<\/p>\n<p>Alhaji Jabaka ya bayyana cewa karamar hukumar ta samu wadatattun magunguna wadanda aka raba su a cibiyoyin lafiya daban-daban domin ci gaba da kula da duk wani sabon lamari na bullar cutar kyauta.<\/p>\n<p>Game da matsalar tsaro a karamar hukumar Maru kuwa, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa ya bayar da umarnin a rika karanta Alkur\u2019ani mai girma a kowace Juma\u2019a da fatan Allah a kawo karshen matsalolin tsaro da suka dade suna addabar yankin.<\/p>\n<p>Ya bayyana fatansa na cewa addu\u2019o\u2019in za su taimaka wa jami\u2019an tsaro wajen yaki da \u2018yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.<\/p>\n<p>Alhaji Jabaka ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa ayyukan raya kasa daban-daban da ya aiwatar a karamar hukumar Maru, musamman gyaran Asibitin Gaba Daya, gina tituna da sauran ayyukan gine-gine.<\/p>\n<p>Ya tabbatar wa da gwamnan da cikakken goyon baya da hadin kan al\u2019ummar Maru domin\u00a0 cigaban\u00a0 Jihar Zamfara.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong><em>Daga Aminu Dalhatu\u00a0<\/em><\/strong><\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al&#8217;ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin. Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan [&hellip;]<\/p>\n","protected":false},"author":15,"featured_media":1955,"comment_status":"closed","ping_status":"closed","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"_jetpack_newsletter_access":"","_jetpack_dont_email_post_to_subs":false,"_jetpack_newsletter_tier_id":0,"_jetpack_memberships_contains_paywalled_content":false,"_jetpack_memberships_contains_paid_content":false,"footnotes":""},"categories":[1,11,4],"tags":[1301,1300,115],"class_list":["post-4923","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-labarai","category-labaran-gida","category-lafiya","tag-kwalara","tag-maru","tag-zamfara"],"jetpack_sharing_enabled":true,"jetpack_featured_media_url":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2024\/06\/zamfara-map-image-edited.jpg","_links":{"self":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4923","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/15"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=4923"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4923\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":4924,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/4923\/revisions\/4924"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1955"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=4923"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=4923"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/radionigeriakaduna.gov.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=4923"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}